Matashi ya bude Kasuwar Hausa ta Duniya a yanar gizo
Wani matashi dan Najeriya mai suna Bello Galadanci, wanda ya yi fice a harkar koyar da hanyoyin ci gaban kasuwanci ga matasa a yanar gizo, a ranar Talatar da ta gabata ya yi nasarar bude sabuwar Kasuwar Hausa ta farko a yanar gizo a duk fadin duniya. Kasuwar ta kunshi cinikayyar motoci da man shafawa […]
Wani matashi dan Najeriya mai suna Bello Galadanci, wanda ya yi fice a harkar koyar da hanyoyin ci gaban kasuwanci ga matasa a yanar gizo, a ranar Talatar da ta gabata ya yi nasarar bude sabuwar Kasuwar Hausa ta farko a yanar gizo a duk fadin duniya.
Kasuwar ta kunshi cinikayyar motoci da man shafawa da atamfofi da zobban azurfa da kayan abinci da kaji, har ma da kulla auratayya a tsakanin samari da ’yan mata. Bayan bude kasuwar ta yanar gizon ce matashin wanda yanzu haka yake zaune a kasar China ya bukaci jama’a su bude shaguna kyauta, don tallata sana’arsu ta yadda za a iya gani a duk fadin duniya, musamman masu amfani da harshen Hausa.
Galadanci ya dauki lokaci yana fayyace irin hanyoyin da ya kamata kananan ’yan kasuwa da wadanda ke sha’awar fara kasuwanci su bi, domin kaiwa ga nasara, inda ya sha yin bayani da amsa tambayoyi kan nasarori da kalubalan da suke tattare da samun nasara a kasuwanci ko akasi.
A shafinsa na yanar gizo ya yi karin haske game da Kasuwar Bello kamar yadda ya sanya mata suna, inda ya ce, “Kasuwar Bello ita ce Kasuwar Hausa ta farko a kan yanar gizo da ke tattara ’yan kasuwa da sana’o’i a wuri guda domin su samu kudi, tare da ba su sababbin dabarun zamani na kasuwanci da gina tattalin arziki.
“Kasuwar Bello tana bai wa ’yan kasuwa hanyoyin samun bayanai a kan kowane irin kaya da ke China da Amurka da ma shiri na musamman domin saye da aikawa zuwa Najeriya da Nijar. Haka kuma kasuwar ta tana bai wa kamfanoni shawarwarin hanyoyin bunkasa harkokinsu da fitar da kaya zuwa kasashen waje,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Kasuwar na da shiri na musamman na samar wa dalibai makarantu da bai wa matasa tallafin karatu zuwa kasashe daban-daban na duniya. Tana kuma koya wa kananan ’yan kasuwa da masu sana’o’i hanyoyi masu sauki na tallata kayayyaki da sana’o’insu a yanar gizo. Bugu da kari kasuwar tana koyar da harsunan kasashen waje ga duk wanda yake sha’awar tafiya kasuwanci.”