Matashi ya caccaki salon siyasar Atiku Abubakar

Wani matashin dan siyasa Hashimu Isah Kwanda, mazaunin Kalaba, Jihar Kuros Riba ya ragargaji takun salon siyasar tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, inda ya bayyana cewa ’yan Najeriya su yi hattara, musamman kan takarar mukamin shugaban kasa da ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takara karkashin inuwar jamiyyar APC. Domin a cewarsa, salo […]

Matashi ya caccaki salon siyasar Atiku Abubakar
Matashi ya caccaki salon siyasar Atiku Abubakar

Wani matashin dan siyasa Hashimu Isah Kwanda, mazaunin Kalaba, Jihar Kuros Riba ya ragargaji takun salon siyasar tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, inda ya bayyana cewa ’yan Najeriya su yi hattara, musamman kan takarar mukamin shugaban kasa da ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takara karkashin inuwar jamiyyar APC. Domin a cewarsa, salo ne na bata wa tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari mai murabus tasa takarar , idan aka yi la,’akari da irin yadda shi tsohon mataimakin shugaban kasar ke watsi da kudi yana sayen wakilan ’yan takara da za su yi zaben fidda gwaninsu a takarar shugaban kasa ta shekarar 2015.

Isah Kwanda, ya yi wancan zargi ne a hirar su da Aminiya, inda ya ce: “ Idan mutane za su iya tunawa kalaman da tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi a shekara ta 2000 lokacin da suka hau mulki, ya ce mutanen Arewa ne suka haddasa yakkin Biyafara, musamman jihohin Kano da Jigawa ne suka kawo koma bayan ci gaban Najeriya, da giyar mulki ta kai shi har ya manta zai nemi shugabancin kasar nan a gaba, to a yanzu mutanen Arewa sun manta ne da maganar da ya fada, ko kuwa yana jin kudin da yake da su ne yana azurta mutane dare daya ne, shi yasa yake jin za su mance su ba shi kuri’ar su su bar Janar Muhammadu Buhari? ”
Ya ce : “Mutanen nan fa da mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya zarga maganar fa ta yi kamari, har sai da aka nada kwamitin wasu manya a Arewa, suka bi gwamnonin da sunan ba su hakuri akan katobarar da ya yi, kamar su dan masanin Kano da Jerimia Useni , akwai marigayi Olusola Sarki da sauran wasu manya irin su Sunday Awoniyi”.
Da aka tambayeshi tunda abuin anyi shi ya wuce, a matsayinsa na dan Arewa ko hakan ya sanya ya gane cewa kalaman da yake zargi Atiku Abubakar ya furta har ma an tura wasu sun bada hakuri a manta da wancan babi a shiga sabo, sai matashin dan siyasar ya ce, ‘kasan zamani imanin wasun mutane yanzu ya kusan komawa kan kudi, amma idan gaskiya suke so jama,’a babu mutumin da ya fi cancanta, kuma yake abinsa don Allah da kuma talaka sai Janar Muhammadu Buhari, domin tunda Buhari ya shiga ANPP bai taba canja jam’iyya ba har aka koma CPC balle yanzu da aka hade aka kafa jam’iyyar APC.
Shi kuma tsohon mataimakin shugaban kasar ba ya siyasar akida, babu mamaki idan bai samu tikitin takara ba ya sake ficewa daga APC ya koma wata jam’iyyar”injishi.
karshe ya bukaci ragowar ’yan takarar mukamin shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC su hakura, su janye wa janar Muhammadu Buhari tun ma kafin akai ga yin zaben fidda gwani
Duk kanin kokarin na ji daga bakin wani mai Magana da yawun dan takarar Alhaji Atiku Abubakar game da zarge –zargen ko shi kansa ya ci tura.