Matashi ya cinna wa kansa wuta a ofishin gwamnati
Sai da ya jike jikinsa jagab kafin ya cinna wa kansa wuta
Wani matashi ya cinna wa kansa wuta, lamarin da ya sa mutane da jami’an tsaro suka yi ta kokarin kashe wutar don ceto rayuwarsa.
Bayan kashe wutar da kyar, jami’an tsaro sun garzaya da mutumin mai shekara 35 asibiti inda ake jinyarsa.
- An kama limami ya daura wa gawa aure a Bauchi
- Sarkin Anka ya mayar da martani kan zarginsa da dakile shirin zaman lafiya
- Matar aure ta kashe budurwar da mijinta zai aura
- Ta yi garkuwa da saurayi saboda ya ki auren ta
Mutumin ya yi danyen aikin ne a ranar Juma’a a wajen ginin Hedikwatar Gwamnati da ke birnin Minsk na kasar Belarus.
Kwamitin Bincike ta kasar ta ce sai da matashin ya jike jikinsa gaba daya da mai kafin ya banka wa kansa wuta.
Hukumar ta ce ta fara bincike domin gano abin da ya tunzura mutumin ya dauki irin wannan mataki a kan kansa.
Bidiyon da aka yada ya nuna mutumin ya ci da wuta yayin da jama’a ke ta tunkaro shi domin kashe wutar.
Kasar Belarus ta jima tana fama da bore tun bayan zaben kasar da ’yan adawa ke zargin an yi murde an ba wa Shugaba mai ci Alexander Lukashenko.
Mista Lukashenko dai ya musanta zargin magudi a zaben.