Matashi ya daɓa wa mahaifiyarsa wuƙa a Bayelsa
Wani matashi mai shekara 22, mai suna Godwin daga unguwar Elebele a Ƙaramar Hukumar Ogbia, a Jihar Bayelsa, ya kashe mahaifiyarsa ta hanyar daɓa mata wuƙa.
Wani matashi mai shekara 22, mai suna Godwin daga unguwar Elebele a Ƙaramar Hukumar Ogbia, a Jihar Bayelsa, ya kashe mahaifiyarsa ta hanyar daɓa mata wuƙa.
Lamarin ya faru ne bayan da ya zarge ta da hana shi yin arziƙi.
- Kotu ta tura Yahaya Bello zuwa Gidan Yari
- Dan Jam’iyyar LP a Majalisar Tarayya ya sauya sheka zuwa APC
Mazauna unguwar sun ce Godwin ya dawo gida kwanaki kaɗan da suka gabata, bayan ya shafe watanni a garin Benin, na Jihar Edo.
Wasu sun ce wani fasto ne ya gargaɗi mahaifiyarsa kan kada ta karɓi kowace irin kyauta daga wajen ɗanta.
Wasu kuma sun ce Godwin, ya dawo gidan da wasu halaye, inda yake iƙirarin cewar an ce mahaifiyar ce ta hana shi yin arziƙi.
Shugaban matasan unguwar Elebele, Kwamared Precious Okala, ya ce lokacin da suka isa wajen, sun tarar da gawar mahaifiyar cikin jini, yayin da matasan unguwar suka kama Godwin suka ɗaure shi.
Ya ce: “Tun da ya dawo daga Benin, ya fara nuna wasu halaye. A ranar da abin ya faru, an ce ya yi faɗa da mahaifiyarsa sannan ya caka mata wuƙa a ciki.
“An ji yana cewa wani ‘Baba’ ya faɗa masa cewa mahaifiyarsa ce ta hana yin arziƙi.”
Kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Musa Mohammed, ya ce an miƙa lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID) don ci gaba da bincike.