Matashi ya fille kan kakarsa ya kai ofishin ’yan sanda

Dattijuwar mai shekara 70 ita ce ci da shan matashin

Matashi ya fille kan kakarsa ya kai ofishin ’yan sanda

Motar da aka dauki gawar dattijuwar a ciki. (Hoto: standardmedia.co.ke)

Wani matashi ya fille kan kakarsa mai kimanin shekara 70 kai, sannan ya wuce da shi kai tsaye zuwa ofishin ’yan sanda.

Jami’an ’yan sanda a babban caji ofis din da ke yankin Kisumu sun cika da al’ajbi bayan da matashin mai shekara 24 ya shiga wurinsu ya nemi su bude bokitin.

Da farko sun dauka abinci ne ya kai wa wasu mutanen da ke tsare a ofishin, amma da suka matsa masa sai ya ce musu kan kakarsa ne a ciki kuma shi ne ya kashe ta.

Bude bokitin ke da wuya, sai suka ga tabbas kan mutum ne sabon yanka a ciki, a ranar Litinin 5 ga watan Afrilu, 2021.

 Nan take suka cukuikuye shi suka kulle, daga baya suka sa shi a gaba ya kai su gidansu inda aka iske gawar tsohuwar kwance cikin jini.

Makwabta a unguwar talakawa ta Nyalenda sun ce ba su san cewa matashin ya aikata danyen aikin ba sai bayan da ’yan sanda suka zo da shi.

Fusatattun makwabtan sun yi yunkurin kwace shi a hannun ’yan sanda su yi masa danyen hukunci; Da kyar ’yan sandan suka samu suka watsa su.

Cikn alhini, jama’a sun yi ta ambaton kirkin dattijuwar da irin fadi-tashin da ta yi ta yi wajen kula da jikan nata wanda goyon kaka ne, kuma ita ke ciyar da shi a tsawon zamansa a wurinta tun yana dan shekara goma sha.

A rahoton na kafar yada labarai ta The Standard, Wani dan unguwar, Dan Okello, ya ce, ko a ranar da abin ya faru, sai da tsohuwar  ta je ta yi sayayya a wani kanti.

“Ta tsufa tukuf, abin takaici ne yadda aka yi mata kisan gilla,” inji shi.

Hotunan lamarin da ya faru a kasar Kenya sun nuna ’yan sandan na  kokarin daukar gawar a wurin da matashin ya yi aika-aikan a unguwar talakawa ta Nyalenda.

A halin yanzu suna tsare da matashin suna gudanar da bincike, amma ba su kai ga cewa komai game da abin da suka gano ba tukuna.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya