Matashi ya hada baki da mahaifiyarsa da fasto sun kashe dalibar jami’a
Wani matashi mai kimanin 23 ya hada baki da mahaifiyarsa da wani limamin coci wadanda ake zargi sun hallaka wata matashiya daliba mai karatu a ajin karshe a jami’ar jihar Legas. Kimanin makwanni biyu ke nan da yarinyar mai suna Favour Daley-Oladele, ta yi sallama da mahaifinta da ke zaune a jihar Osun, inda ta […]
Wadanda ake zargi
Wani matashi mai kimanin 23 ya hada baki da mahaifiyarsa da wani limamin coci wadanda ake zargi sun hallaka wata matashiya daliba mai karatu a ajin karshe a jami’ar jihar Legas.
Kimanin makwanni biyu ke nan da yarinyar mai suna Favour Daley-Oladele, ta yi sallama da mahaifinta da ke zaune a jihar Osun, inda ta shaida masu zata koma makaranta Legas amma zata biya wajen saurayinta da ya kira ta a waya wanda shima a baya dan jami’ar ne wanda suka hadu watanni uku da suka shude, tun bayan da ta bar gida ba a sake jin duriyarta ba.
A yau Lahadi ne a ka gano gawar yarinyar a yankin Mowa a jihar Ogun, yayin da jami’an ‘yan sandan jihar suka kame wadanda ake zargin da suka hadar da saurayin mai suna Adeeko Owolabi da mahaifiyarsa da kuma faston Segun Philip, da ake zargi da hannun da kisan.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeye, ya shaida wa Aminiya cewa, matashin ya shaida masu cewa yarinyar budurwarsa ce, kuma ya hada baki da faston da mahaifiyarsa sun kashe ta ne domin su yi tsafi da ita.