Matashi ya hallaka mahaifiyarsa da duka a Bauchi
Kwamishinan ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wanda ake zargin a kotu.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta cafke wani matashi Safiyanu Dalhatu, mai shekara 20, kan zargin kashe mahaifiyarsa har lahira a unguwar Abujan Kwata.
Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ’yan Kwamitin Tsaro na Unguwar ne suka kai rahoton lamarin ofishin rundunar na ‘A’ Division da ke Bauchi.
- Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio
- Babu abin da zai hana mu zama jam’iyya ɗaya da Kwankwaso — Shekarau
Bincike ya nuna cewar mahaifiyar matashin, Salama Abdullahi, mai shekara 40, ta samu karaya a hannayenta biyu sakamakon dukan da ya mata bayan sun samu saɓani.
Bayan samun rahoto, jami’an rundunar ƙarƙashin jagorancin CSP Abdullahi Muazu, sun garzaya wajen da lamarin ya faru.
Sun kai Salama Asibitin ATBUTH da ke Bauchi, amma daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarta.
Bincike ya nuna cewa matashin ya yi amfani da wani abu wajen dukan mahaifiyar tasa.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin.
Kuma ya ce da zarar bincike ya kammala, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.