Matashi ya hallaka tsoho mai shekara 75 a Kazaure

Ana zargin wani matashi a garin Kazaure da ke Jihar Jigawa mai suna Ibrahim Adamu wanda dan yayar shugaban karamar Hukumar Kazaure ne kuma dan uwa ga dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kazaure da Roni Alhaji Bashir Adamu Jimbo da hallaka wani tsoho mai shekara 75 mai suna Ado Kandare da ke gadi a […]

Matashi ya hallaka tsoho mai shekara 75 a Kazaure
Matashi ya hallaka tsoho mai shekara 75 a Kazaure

Ana zargin wani matashi a garin Kazaure da ke Jihar Jigawa mai suna Ibrahim Adamu wanda dan yayar shugaban karamar Hukumar Kazaure ne kuma dan uwa ga dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kazaure da Roni Alhaji Bashir Adamu Jimbo da hallaka wani tsoho mai shekara 75 mai suna Ado Kandare da ke gadi a kusa da gidansa a daren Juma’ar da ta gabata.

Majiyarmu ta ce matashin ya nemi marigayi Ado Kandare ne ya ba shi mafaka saboda ’yan uwansa suna neman hallaka shi, bayan sun sace masa ’ya’ya, kuma sun rufe masa gida da kwado ta waje, lamarin da ya sa ya sa marigayin ya ba shi wuri ya shimfida tabarma a dakin da Ado yake kwance tare da dan kanensa.
dan kanen marigayin mai suna Abdulrahaman ya ce suna kwance da misalin karfe 4:30
na asuba sai ya ji wanda ake zargin yana tashin Malam Ado Kandare ya raka shi gida su balle kofar gidansa da ’yan uwansa suka kulle.
“Bayan sun fita sai na koma na kwanta, can bayan gari ya fara wayewa sai na fito domin na ga yayan mahaifina bai dawo ba, sai kawai na gan shi a cikin jini male-male an farfasa masa kai kuma ga alama an kwakule masa ido, shi ne na garzaya gidanmu na sanar da mahaifina halin da yake ciki,” inji shi.
Zuwan kanen marigayin Malam Isa Abubakar ya lura rai ya yi halinsa, inda ya sanar da jami’an tsaro, amma har misalin karfe 8:00 na safe babu wanda ya kula gawar marigayin saboda mutane na tsoron fada wa hukuma kasancewar wanda ake zargin yana da ’yan uwa manya.
Malam Isa ya ce, wani abin mamaki tun ba a je ko’ina ba sai aka fara alakanta wanda ake zargin da cewa yana da tabin hankali don a ba shi kariyar da zai kubuta daga hukunci.
Malam Isa ya kara da cewa babu yadda za su yi sun mika komai ga Allah domin Shi ne gatansu babu wanda zai taimake su a cikin lamarin.
Uban gidan marigayi Ado wanda hakimi ne a Masarautar Kazaure da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce ya san Ado tun yana karami amma alakarsu ta fara ne kimanin shekara biyar da suka gabata.
Ya ce a tsawon zamansa da Ado bai taba jin abokin fadansa ba, kuma ya ce zai yi bakin kokarinsa wajan nema wa iyalan marigayin hakkinsu ta fuskar shari’a.
Ya ce yanzu magana tana gaban ’yan sanda suna bincike, saboda haka sun tsaya su ga sakamakon bincikensu kafin su san irin matakin da za su dauka a kan maganar.
Shugaban karamar hukumar Alhaji Abubakar Sadik Mabo ya ce wanda ake zargin yana da tabin hankali, kuma ya tabbatar da cewa an tsinci gawar Ado ne a kofar gidan Ibrahim.
Mabo ya yi soki yadda wasu ’yan siyasa suke amfani da lamarin wajen cin mutuncinsu da bata musu suna, saboda wanda ake zargin yana da alaka da su.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa DSP Audu Jinjiri ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma wanda ake tuhumar yana hannunsu suna bincike da zarar sun kammala za su gabatar da shi a gaban kotu.

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 da sace dabbobi a Katsina  

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista