Matashi ya kafa dakin girkin tafi-da-gidanka a Saudiyya

Wani matashi dan Saudiyya mai shekara 25 ya bunkasa harkar kasuwancinsa a dakin girki na tafi-da-gidanka. Matashin mai suna Mamdouh Al-Mousa, ya kana sahfe sa’o’i 12 yana hada-hadar raba amutane abinci a titunan birnin Riyadh, inda su kuma ke jinka masa awalaja. Labarin matashi Mamdouh Al-Mousa da dakin girkinsa na tafi-da-gidanka ya baibaye kafofin yada […]

Matashi ya kafa dakin girkin tafi-da-gidanka a Saudiyya
Matashi ya kafa dakin girkin tafi-da-gidanka a Saudiyya

Wani matashi dan Saudiyya mai shekara 25 ya bunkasa harkar kasuwancinsa a dakin girki na tafi-da-gidanka. Matashin mai suna Mamdouh Al-Mousa, ya kana sahfe sa’o’i 12 yana hada-hadar raba amutane abinci a titunan birnin Riyadh, inda su kuma ke jinka masa awalaja.

Labarin matashi Mamdouh Al-Mousa da dakin girkinsa na tafi-da-gidanka ya baibaye kafofin yada labarai na kasar, inda suka bayyana yadda yake kai kawo a kan titin Sarki Abdullah da ke birnin Riyadh, kuma matafiya na baibaye da shi.
Mamdouh Al-Mousa ya ce ya sayi wannan dakin girkin ne mai tayoyi, sai da abokinsa, don su rika amfnai da shi a lokacin da ba sa yin komai, ko suke hutawa, amma sai abokinsa ya shawarce shi da ya mayar da shi dakin girkin tafi-da-gidanka, don ya rika sayar da shayi da nau’;ukan abinci mai dumi. “Na hada wannan kasuwancin ne tare da wasu abokaina su biyu,” inji shi.
Ya ce ya kashe Riyal dubu 55, wato daidai da Naira 3,300,000 wajen samar da kayan aiki a dakin girkinsa.
“Mun fara da sayar da shayi da rowan abinci mai dumi, kuma kowa na son abin da muke yi, daga nan muka kara yawan lokutan sana’armu zuwa sa’o’i 12, inda mutum uku ke kula da masu sayen kayan mu,” inji shi.
Wannan dakin girki na tafi-da-gidanka yana da tayoyi, wadanda ke makale a jikin mota.
“Cinikinmu ya tashi daga Riyal Dubu daya zuwa uku (Naira dubu 60 zuwa 180) a kowace rana,” a cewarsa, inda ya yi karin haske da cewa: “Abokan huldarmu da suka kasa biyan kudin abin sha mukan ba su kyauta.”
“Kuma akwai wasu masu sayen kayan da ke ba mu kudin da ya wuce na abin da suka saya, shi yasa suke umartarmu mu rika bayar da kyautar abin shag a mabukata,” inji shi.