Matashi ya kashe abokinsa da adda a Kuros Riba

An ruwaito cewa lamarin ya samo asali ne daga saɓanin da ya shiga tsakaninsu kan wata harka ta kasuwanci.

Matashi ya kashe abokinsa da adda a Kuros Riba

Wani matashi mai suna Micheal Ndifon, mai kimanin shekara 42, ya kashe abokinsa, Charles Ekuma Eze, mai shekara 36, bayan ya sare shi da adda a garin Ikom da ke Jihar Kuros Riba.

Aminiya ta tattaro cewa lamarin ya samo asali ne daga saɓanin da ya shiga tsakaninsu kan wata harka ta kasuwanci, wanda ya rikiɗe zuwa faɗa.

Rahotanni sun ce bayan musayar yawu da suka yi, Micheal cikin fushi ya ɗauko adda ya bi Charles da nufin kai masa hari.

Duk da cewa marigayin ya yi ƙoƙarin guje wa harin, amma wanda ake zargin ya cim masa ya sare shi a kai.

Bayanai sun ce sakamakon raunukan da ya samu, Charles ya faɗi ƙasa warwas, inda ya rasu kafin a kai masa ɗauki.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kuros Riba, SP Sunday Eitokpa, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin.

Ya ce an kama Micheal Ndifon, kuma yana tsare a ofishin ‘yan sanda da ke Ikom yayin da ake ci gaba da bincike.

A cewarsa, da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa tanadin doka.