Matashi ya kashe abokinsa da kwalba

Ana tuhumar wani matashi dan shekara 23, mai suna Okon Aniedi da kashe abokinsa na kut-da-kut mai suna Daniel Obot ta hanayar dava masa kwalba saboda yana zarginsa da sace masa wayoyin salula guda uku.Wannan lamari ya auku ne a kauye Ekpiri Obutong a karamar Hukumar Akpabuyo ta Jihar Kurosr Riba. A cewar Aniedi, abokin […]

Matashi ya kashe abokinsa da kwalba
Matashi ya kashe abokinsa da kwalba

Ana tuhumar wani matashi dan shekara 23, mai suna Okon Aniedi da kashe abokinsa na kut-da-kut mai suna Daniel Obot ta hanayar dava masa kwalba saboda yana zarginsa da sace masa wayoyin salula guda uku.
Wannan lamari ya auku ne a kauye Ekpiri Obutong a karamar Hukumar Akpabuyo ta Jihar Kurosr Riba. A cewar Aniedi, abokin nasa ya zo har gida ya kwashe masa wayoyinsa na hannu ya je ya sayar.
A bayaninsa cikin nadama da ya yi wa Aminiya, wanda ake zargin ya ce: “Duk lokacin da na bukaci ya ba ni wayoyina ko kudi sai ya yi min barazanar zai kashe ni, sai ya sare ni da adda in mutu. Ni kuma da na ga da gaske yake yi, ya dauko adda ya nufo ni, sai na fasa kwalba na dava masa ita a kirjinsa; alhalin ni da shi abokan juna ne, barci kadai yake raba mu.”
Matashin dai ya nuna nadama bisa abin da ya aikata.