Matashi ya kashe farkan matar babansa a Kalaba

A Larabar da ta gabata ce rundunar ’yan sandan Jihar Kurosriba ta gabatar wa manema labarai wani matashi mai matsakaicin shekaru, mai suna King Akpanke da ake zargi da kashe farkan matar babansa, sakamakon zarginsa da yake yi na lalata da matar mahaifin nasa.A bayanin da ya yi wa Aminiya, wanda ake zargi da aikata […]

Matashi ya kashe farkan matar babansa a Kalaba
Matashi ya kashe farkan matar babansa a Kalaba

A Larabar da ta gabata ce rundunar ’yan sandan Jihar Kurosriba ta gabatar wa manema labarai wani matashi mai matsakaicin shekaru, mai suna King Akpanke da ake zargi da kashe farkan matar babansa, sakamakon zarginsa da yake yi na lalata da matar mahaifin nasa.
A bayanin da ya yi wa Aminiya, wanda ake zargi da aikata laifin kisan, Akpanke ya ce: “Ba tun yau ba na gargadi mutumin da ya daina shigowa gidanmu yana fasikanci da wannan mata. Na yanke shawarar yanke hukuncin kashe mutumin ne, domin in kare martabar gidanmu. Na sha ja masa kunne ya daina zuwa, ya ki.
Daga karshe ma har rika zuwa ya yi yana zagina, muka kaure da fada, ya dauko sanda yana dukana. Ni kuma na shiga daki na dauko wuka na farke masa ciki, daga bisani na ga ashe har ma sanadin haka ya mutu.”
Sai dai kuma ’yan sandan sun sakaya wa manema labarai sunan wanda aka kashen. A yayin da suka ce nan ba da jimawa ba, idan sun gama bincike za su mika shi kotu.
A wannan ranar, Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kurosriba, Mista Henry Fadairo ya gabatar wa ’yan jarida karin wasu matasa ’yan kungiyar asiri ta Skylo da kuma ’yan fashi. Su ma ya ce nan gaba kadan ne za a gabatar da su gaban kotu, bayan sun gama bincikensu.