Matashi ya kashe Fasto a kan itacen Naira 500

Wani matashi mai kimanin shekara 32 mai suna Anya Onah ya shiga hannun ’yan sanda a Jihar Nasarawa sakamakon zarginsa da kashe wani fasto mai suna Fasto Zakariya Joseph Kura a kan itacen Naira 500.Lamarin wanda ya auku a garin Obi hedikwatar karamar Hukumar Obi da ke jihar an ce Anya Onah ya sassare Fasto […]

Matashi ya kashe Fasto a kan itacen Naira 500
Matashi ya kashe Fasto a kan itacen Naira 500

Wani matashi mai kimanin shekara 32 mai suna Anya Onah ya shiga hannun ’yan sanda a Jihar Nasarawa sakamakon zarginsa da kashe wani fasto mai suna Fasto Zakariya Joseph Kura a kan itacen Naira 500.
Lamarin wanda ya auku a garin Obi hedikwatar karamar Hukumar Obi da ke jihar an ce Anya Onah ya sassare Fasto Zakariya Joseph Kura ne a cikin daji.
Da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a Lafiya, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Lawal Shehu ya ce binciken da jami’ansa da aka turo inda lamarin ya auku suka yi kuma suka kama wanda ake zargin ya nuna cewa lamarin ya auku ne a lokacin da marigayi Fasto Zakariya, faston cocin Ecwa da ke Obi kuma shugaban kungiyar Kiristocin (CAN) a karamar hukumar ya tafi daji don ya faskara wani itace da aka kada shi a dajin.
Kwamshinan ya ce yana cikin faskara itacen ne sai Anya Onah ya je ya tambaye shi wa ya ba shi izinin ya faskara itacen. Sai Fasto Zakariya ya ce masa wani mamban cocinsa ne ya ce masa ya je ya sare itacen ya yi amfani da shi.
Ya ce Anya Onah ya nuna masa cewa itacensa ne ya saya daga wurin wani mutum a kan Naira 500, sai Fasto Zakariya ya ce ba damuwa su je gida zai ba shi kudin don ba ya son rikici, amma sai Anya ya ki amincewa, ya ce wa faston ba ya bukatar kudin, itacensa da faston ya fara faskarewa yake so ya mayar da shi yadda ya same shi.
Ya ce a nan ne suka samu rashin jituwa sakamakon nacewar da Anya ya yi cewa Fasto Zakariya ya mayar da itacensa yadda ya tarar da shi, kuma kafin a ankara sai wanda ake zargin ya sa addar da ke hannusa ya sassare faston sai da ya mutu nan take.
Kwamishinan ’Yan sandan ya ce wadansu mambobin cocin marigayin da suka samu labarin aukuwar lamarin ne suka sanar da jami’ansa wadanda suka shiga dajin suka kama wanda ake zargin. Kuma ya ce za su gurfanar da shi a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.
Sai dai a zantawarsa da manema labarai, Anya Onah ya musanta zargin inda ya ce bayan da marigayi Fasto Zakariya ya ba shi hakuri cewa idan sun tafi gida zai ba shi kudin ya hakura ya bar faston a daji ya koma gida, daga bisani ne ya samu labarin mutuwar faston. Ya ce da ya tambayi wanda ya sanar da shi mutuwar faston sai ya gaya masa cewa wadansu Fulani makiyaya su biyu ne suka kashe shi.