Matashi ya kashe gwaggonsa a Uyo

Wani matashi mai suna Daniel Michael Edet, dan shekara 19 da haihuwa, dan kauyen Idoro yankin birnin Uyo, da ke karamar Hukumar Uyo Jihar Akwa Ibom ya kashe gwaggonsa mai suna Glory Edet Ebere ta hanyar daba mata wuka.  Da yake gabatar da matashin ga manema labarai a hedkwatar rundunar ’yan sandan jihar, Mataimakin Kwamishinan […]

Matashi ya kashe gwaggonsa a Uyo
Matashi ya kashe gwaggonsa a Uyo

Wani matashi mai suna Daniel Michael Edet, dan shekara 19 da haihuwa, dan kauyen Idoro yankin birnin Uyo, da ke karamar Hukumar Uyo Jihar Akwa Ibom ya kashe gwaggonsa mai suna Glory Edet Ebere ta hanyar daba mata wuka. 

Da yake gabatar da matashin ga manema labarai a hedkwatar rundunar ’yan sandan jihar, Mataimakin Kwamishinan ’yan sandan mai kula da sashen aikata miyagun laifuka, Mike Okolikamun ya ce kama wanda ake zargin shi ne gawurtaccen kamu da suka yi a tsakanin nan. Da yake karin haske game da yadda aka yi har matashin ya kashe gwaggon tasa, ya ce: “Ranar 11 ga watan jiya ce matashin ya yanke shawarar dawowa gidanta ya ci gaba da zama da ita, suna zaune lafiya babu wanin rikici tsakaninsu; har ya shirya ya ce mata ya tafi aiki. Daga baya kuma sai ya dawo ya daba mata wuka, ta fadi shame-shame cikin jinni, babu mataimaki har sai da makwabtanta suka ji tana ihu na neman a taimako. Suka garzayo gidan suka iske halin da suka same ta, shi kuma ya sulale ya gudu.”
Ya ci gaba da karin haske yana cewa: “Bayan da ya yi nasarar kashe ta sai ya dauki gawarta ya sanya cikin motarta shi da rakiyar wasu abokansa za su je su jefar da gawar wani wuri da zaton su ba za a iya ganewa ba. Shi ne ’yan sintiri da ke wurin suka gan su, suka bi su domin ganin abin da za su yar a wurin. Shi ne suka ranta cikin na kare, su kuma ’yan sintiri suka suka kama su a wannan dare, suka kawo su har gidan su Daniel”
Bayan ’yan sanda sun tsananta bincikensa ne ya furta masu cewa shi ya kasha ta saboda ya nemi ta ba shi kudi ta hana shi.