Matashi ya kashe gwaggonsa mai shekaru 99 kan cacar Baba Ijebu
Cacar Baba Ijebu daya ce daga cikin nau’o’in cacar loto da ake amfani da lambobi wacce kuma ta shahara a Kudancin kasar nan. Wani mutum da ake kira Baba Ijebu ne ya assasa ta, sai dai a dalilinta wani matashi ya kashe ’yar uwan mahaifinsa mai shekara casa’in da tara. A cewar Mai magana da […]
Cacar Baba Ijebu daya ce daga cikin nau’o’in cacar loto da ake amfani da lambobi wacce kuma ta shahara a Kudancin kasar nan. Wani mutum da ake kira Baba Ijebu ne ya assasa ta, sai dai a dalilinta wani matashi ya kashe ’yar uwan mahaifinsa mai shekara casa’in da tara.
A cewar Mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi matashin ya shiga hannun ’yan sanda ne bayan da wadansu mutane suka kira babban jami’in ’yan sandan yankin Ago-Iwoye CSP Ade Adedoyin suka sanar masa cewa wani matashi ya hallaka yayar mahaifinsa lamarin da ya sanya shi tura jami’an ’yan sanda suka kama wanda ake zargin mai suna Owolabi Folorunso dan shekara 29.
“ An kama wanda ake zargin da addar da ya dadatsa yayar mahaifinsa mai suna Ebunola Aroboto, inda ya kashe ta, kuma ya amsa laifinsa lokacin da muka bincike shi. Ya ce ya yi zargin ’yar uwan mahaifin nasa ce take hana masa sa’a a cikin lamuransa na yau da gobe. Ya ce shi mai yawan buga cacar Baba Ijebu ne kuma duk sa’ar da ya buga loton da ya kamata ya ci makudan kudi sai gwaggon tasa ta yi amfani da maita ta juya lambobin cacar, abin da yake hana shi nasara, kuma lamarin da ya sanya shi ya kashe ta domin ya huta,” inji DSP Abimbola Oyeyemi.
Ya ce an kai gawar matar dakin ajiyar gawa na Babban Asibitin Ijebu-Ode, don ci gaba da bincike, “Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun Ahmed Iliyasu ya umarci mataimakinsa da ke kula da sashen binciken manyan laifuffuka, Wale Abbas ya ci gaba da bincikar lamarin kafin a gurfanar da wanda ake zargin a kotu” inji shi.