Matashi ya kashe kakansa da fartanya a Borno
Matashi ya buga wa kakansa mai shekaru 90 fartanya a kai ya hallaka shi
’Yan sandan sun kama wani matashi kan zargin sa da laifin kashe kakansa dan kimanin shekaru 90 a Jihar Borno.
An zargin matashin ya buga wa kakan nasa fartanya a kai ne a Karamar Hukumar Kwaya-kusar da ke jihar.
ASP Kenneth Daso, ya ce sun cafko wanda ake zargin aka tsare shi a ofishin rundunar da ke Maiduguri ranar Alhamis kuma zargin a kotu bayan an kammala bincike.
Haka nan rundunar ta gabatar da wata mata da ta kashe mijinta a garin Chibok, sakamakon rikicin da ya barke tsakaninsu.
- NAJERIYA A YAU: Alaƙar Da Ke Tsakanin Masu Haƙar Ma’adanai Da ‘Yan Bindiga
- ‘Dalilin da ba a samun isasshiyar wutar lantarki a Nijeriya’
Ta amsa laifin da ta aikata, inda ta ce ta kasa danne zuciyarta ne bayan mijin nata ya lakada wa danta duka.
Har ila yau, rundunar ta gurfanar da wasu mutane tara da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, da suka hada da kisan kai, barna, satar kayayyakin more rayuwa, cin zarafi, da kuma ta’ammali da muggan kwayoyi.
Abubuwan da aka gano sun haɗa da fartanya, gatari, ƙwayoyi, da kuma dukiyar da aka sace.
Haka nan rundunar ta kuma tabbatar da cewar, ta ceto wasu ‘yan mata 23 da ake kokarin safarar su don yin karuwanci a Jihar Delta.
ASP Daso ya gargadi masu aikata laifuka da su daina ko kuma su fuskanci fushin doka, inda ya jaddada kudirin rundunar na tabbatar da tsaro da tsaro a jihar Borno.
“Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta Daura damarar ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro a Jihar.”