Matashi ya kashe kakansa da kawunsa

Rundunar ta ce tana gudanar da bincike kan musababbin da ya sa matashin ya aikata laifin.

Matashi ya kashe kakansa da kawunsa

’Yan sanda sun kama wani matashi kan zargin kashe kakansa da kuma kawunsa a yankin Apete da ke Ibadan a Jihar Oyo.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo, SP Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamari cikin wani saƙo da ya aike wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Litinin.

Osifeso ya ce, “An fara gudanar da bincike kan lamarin, za a fitar da bayanan da suka dace idan aka kammala bincike.”

Ya ƙara da cewa, ’yan sanda suna aiki don gano dalilin da ya sa matashin ya aikata laifin.

Ya ce da zarar sun kammala bincike za su sanar da jama’a halin da ake ciki.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Lahadi.

Wanda ake zargin, mai suna Ahmed, na zaune a gidansu tare da mahaifinsa wanda makaho ne da kuma kawunsa wanda ke fama da rashin lafiya.

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo