Matashi ya kashe kanensa, ya raunata daya
A ranar Alhamis din makon jiya ne wani matashi mai shekara 25, mai suna Kabiru Zubairu ya kashe kanensa mai suna Rabi’u Zubairu mai shekara 23 ta hanyar daba masa wuka a kirji saboda wata ’yar hatsaniya da ta auku a tsakaninsu a gidansu da ke Unguwar Hayin dan Mani da ke Kaduna. Kabiru ya […]

A ranar Alhamis din makon jiya ne wani matashi mai shekara 25, mai suna Kabiru Zubairu ya kashe kanensa mai suna Rabi’u Zubairu mai shekara 23 ta hanyar daba masa wuka a kirji saboda wata ’yar hatsaniya da ta auku a tsakaninsu a gidansu da ke Unguwar Hayin dan Mani da ke Kaduna.
Kabiru ya kuma yanki wani kanensa mai suna Yunusa dan shekara 21 da wukar a lokacin da ya yi kokarin taimaka wa mamancin. Ana zargin Kabiru da shaye-shaye wanda hakan ya sa ya samu tabin hankali.
Mahaifinsu Malam Zubairu Umar mai shekara 70, ya shaida wa Aminiya cewa. “Na dauki kaddara kan abin da ya faru. Ya yi shekaru kusan uku ba ya aikin komai, daga baya sai ya fara sayar da mangoro, kafin ya koma sayar da rake. Abin da ya faru a wannan rana shi ne marigayin da abokansa sun je bude kofarsu ta waje sai suka ture masa kayan rakensa shi ke nan sai haukarsa ta motsa ya dauki wuka yana zage-zage, har ta kai ga kashe kanensa.”
Shi kuwa Yunusa wanda Kabiru ya daddaba masa wuka a fuska da hannu da bayansa ya ce,”Ina zaune a kofar wani gida, sai na hango Kabiru ya kai yanka da wuka a bakin kofa, sai na yiwo gida domin ganin me ke faruwa. Da na iso na iske yana zage-zage, ban ce masa komai ba na wuce cikin gida na tarar Rabi’u zai fita waje. Na shiga daki ke nan sai na ji hatsaniya a waje, ina fita sai na tarar da Rabi’u ya rike kirjinsa, Kabiru ya daba masa wuka. Ganin haka sai na rike Rabi’u domin in taimaka masa. Sai Kabiru ya yiwo kaina zai daba min wukar, na samu sanda na maka masa. Ya sake kawo min yanka ban san ya yanke ni ba, sai da mutane suka fada min.”
Rabi’u ya rasu ne a gidansu kafin a kai shi asibiti a yayin da aka kai Yunusa wani kyemis da ke kusa domin a tsayar da jinin da ke kwarara daga jikinsa.Wanda ake zargin yanzu haka yana hannun ’yan sanda bayan matasan unguwar da ake kira ’yan majalisa sun taimaka aka kama shi.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Aminu Lawan ya ce tuni an fara binciken kan al’amarin.