Matashi ya kashe kansa a gasar shan taramol
A ranar Litinin da ta gabata ce mazauna Unguwar Rama da ke bayan Bankin Diamond a garin Keffin ta Jihar Nasarawa, suka yi yammaci cikin takaici sakamakon rasuwar wani matashi a yankin bayan ya sha kafson din taramol 12 a lokaci guda.Wata majiya ta kusa da marigayin ta bayyana wa Aminiya cewa matashin mai suna […]
A ranar Litinin da ta gabata ce mazauna Unguwar Rama da ke bayan Bankin Diamond a garin Keffin ta Jihar Nasarawa, suka yi yammaci cikin takaici sakamakon rasuwar wani matashi a yankin bayan ya sha kafson din taramol 12 a lokaci guda.
Wata majiya ta kusa da marigayin ta bayyana wa Aminiya cewa matashin mai suna Obed Africa ya gamu da ajalinsa ne bayan da ya sha taramol 12 da misalin karfe 10 na safe a lokacin da suka yi musu da abokansa cewa ba zai iya hadiyar kwayoyin 12 a lokaci guda ba.
Marigayin da wasu abokansa sun yi musu ne har ya yi zafi, inda a cikin raha wani daga cikin abokan ya ce ya sanya wayarsa idan marigayin ya iya shanye kwayoyin 12 wayar ta zama tasa. Kuma daga bisani wani daga cikinsu ya sanya Naira 200 kacal wanda hakan ya karfafa wa Obed gwiwa aka aika aka sayo kwayoyin.
Majiyar ta ce ganin marigayin ya himmatu zai sha kwayoyin, wasu daga cikin abokansa da suka san illar kwayar taramol sun kwabe shi cewa kada ya sha, amma ya yi kunnen uwar shegu ya shanye duka.
Majiyar ta ce, bayan Obed ya shanye kwayoyin, kuma ya cafki kudinsa Naira 200 ya sa a aljihu, sai suka watse kowa ya ci gaba da harkokinsa.
Majiyar ta ce da misalin karfe 2:00 na rana, bayan kwayar ta gama narkewa a jikin Obed, sai jikinsa ya rikice inda tilas aka kwashe shi zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Keffi, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
Bayan an dawo gida da gawar Obed, iyayensa sun nuna ba su gamsu cewa dansu ya rasu ba, wanda hakan ya sa suka bai wa wani jami’in kiwon lafiya damar sake duba gawar a gida, kuma a karshe ya nuna musu cewa da alama numfashi bai gama rabuwa da gangar jikin Obed ba. Majiyar ta ce jin haka sai aka sake garzayawa da shi wani asibiti mai zaman kansa inda a can ma aka sake tabbatar da rasuwar Obed.
Majiyar wadda ta nemi a sakaye sunanta, ta ce haka iyayen Obed suka rungumi kaddara kan mutuwar dansu.
Majiyar ta ce washegari Talata an ga ’yan sanda sun ziyarci gidan su marigayin bayan da labari ya isa gare su don sanin halin da ake ciki.
Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan jihar Nasarawa DSP Umaru Isma’ila, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce Obed ya sha taramol ne kuma suna nan suna gudanar da bincike a kan lamarin.
Tuni aka yi jana’izar marigayin a makabartar Kirista kamar yadda addinin Kirista ya tanada.