Matashi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa da tabarya

Ya yi yunkurin kashe matar da guba amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Matashi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa da tabarya

‘Yan sanda

Rahotanni na cewa wani matashi ya kashe kishiyar uwarsa da tabarya a garin Ihima Obeiba Ebozohu da ke Karamar Hukumar Okehi a Jihar Kogi.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa, matashin mai suna Idris Aminu ya samu nasarar kashe kishiyar mahaifiyarsa a gidansu yayin da take sharar barci a daren ranar Lahadi.

Mazauna yankin sun bayyana cewa tun kwanaki uku da suka gabata matashin ya yi yunkurin kashe matar mai suna Salamotu Aminu da guba amma a wannan karo hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Mai Magana da Yawun ’Yan sandan Jihar Kogi, SP William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin.

SP Aya ya ce an gano taɓaryar da ake zargin matashin ya yi amfani da ita wajen kashe matar da ya boye a dakinsa bayan an tsananta bincike.

Ya ci gaba da cewa, daya daga cikin ’ya’yan matar ne mai suna Ibrahim Aminu ya yi arba da gawar mahaifiyarsa tsamo-tsamo a cikin jini, lamarin da ya sanya nan da nan ya ankarar da mahukunta mafi kusa.

Jami’in ya ce tuni sun cika hannu da wanda ake zargin yayin da bincike zai ci gaba da gudana kuma da zarar an kammala za a mika wa Kuliya lamarin.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya