Matashi ya kashe magidanci wajen sayen kunun aya
Wani matashi da ake kyautata zaton dan daba ne mai suna Abubakar Ibrahim, wanda shekarunsa ba su haura 16 ba, ya kashe wani magidanci mai suna Malam Haruna Abdullahi a cikin dakinsa a unguwar Limawa ‘A’ da ke karamar Hukumar Chanchaga a Jihar Neja. Binciken Aminiya ya nuna cewa matashin, wanda ya kammala karamar sakandaren […]


Wani matashi da ake kyautata zaton dan daba ne mai suna Abubakar Ibrahim, wanda shekarunsa ba su haura 16 ba, ya kashe wani magidanci mai suna Malam Haruna Abdullahi a cikin dakinsa a unguwar Limawa ‘A’ da ke karamar Hukumar Chanchaga a Jihar Neja.
Binciken Aminiya ya nuna cewa matashin, wanda ya kammala karamar sakandaren gwamnati ta Maitumbi da ke karamar Hukumar Bosso, ya yi aika-aikar ce a tsakanin karfe 10 zuwa 11 na dare, inda ya iske marigayin tare da matarsa da kuma ’ya’yansu 3, yana ikirarin wani abokin wansa, wanda aka fi sani da sunan dan Asabe ko kuma Mai Kalos ne ya aike shi sayen kunun aya a gidan marigayin.
Yayin da take wa Aminiya bayani, matar marigayin, Malama Hadiza ta ce, “Mun kwanta ke nan, aka yi sallama har sau biyu, ba mu amsa ba, sai kawai (wanda ake zargin) ya bude kofa ya shigo. Sai shi marigayi ya rike shi, ya ce, ‘Yaya aka yi ka shigo bayan ka yi sallama ba a amsa ba?’ Ya ce, an aiko shi ne sayen kunun aya. Maigidana ya ce, ‘Tunda an aiko ka sayen kunun aya, ka yi sallama ba a amsa ba, ai sai ka tsaya. Kai barawo ne, ba kunun aya ka zo saye ba’. A nan ne ya ce, Mai Kalos ne ya aiko shi sayen kunun aya. Shi ne maigidana ya ki kyale shi.
“Da ya lura cewa marigayin ba shi da niyyar kyale shi ne, sai ya kama shi da kokawa daga falo har zuwa uwar daka. Suna cikin uwar daka ne, sai shi Abubakar ya ciro wuka ya fara daba wa marigayin a sassa daban-daban na jikinsa. Ina ganin haka, sai na fito waje ina ta ihu, domin jama’a su kawo agaji. Da na ga yana neman hallaka mini miji, shi ne na nemo tabarya na yi ta dukansa da shi, amma saboda taurin ransa, ya ki rabuwa da shi, har suka fito waje, jini yana ta zuba babu kakautawa. Lokacin da suka fito waje ne, maza suka rirrike shi (Abubakar) don kar ya gudu”. Inji ta.
Malama Hadiza ta ce lamarin sai ya zame mata tamkar a mafarki, domin ko da ta ga jama’a na kai-komo, kuma ta ga jami’an tsaro, sai jikinta ya ba ta cewar mijinta ya rasu.
Malam Mahmud Abdullahi, wanda makwabcin marigayin ne da suke cikin gida daya ya shaida wa wakilin Aminiya cewa yana kwance ne a daki bai dade da dawowa daga aiki ba, ya ji kuwwa ana ihu barawo. “Na fito, zan shiga dakin ke nan, sai na ji marigayin yana cewa, ‘Yana tare da wuka’, matar kuma tana cewa, ‘Wayyo, zai kashe mini shi’. Sai na koma na nemo katako, fitowar da zan yi, sai na yi karo da su, marigayin ya rungume shi, wukar ta fadi, sai na jefar da katakon da ke hannuna, marigayin ya danka mini shi, ni kuma na rike shi (Abubakar). Shi kuma (marigayin) ya fadi.
“Ana haka, sai ga maigidanmu Malam dantani, sai kuma mutane suka taru, sai shi (Abubakar) ya kama cewa, ‘Wallahi ni babu ruwana, Mai Kalos ne ya turo ni’. Sai aka fita neman motar da za ta kai marigayin asibiti, bayan kamar minti 30 aka samu, lokacin ma mun ga kamar ba ya motsi, amma don mu tabbatar muka kai shi asibiti, inda muna zuwa aka ce ya cika, kafin mu kawo shi”.
Malama Mardiyya Ahmad, wadda ke makwabtaka da in da abin ya faru, ta kuma shaida wa wakilinmu, cewa shi yaron ya shiga gidaje biyu yana sallama. Bayan da ya fito daga gida na biyun ne ya kebe gefe guda yana waya akai-akai, aka yi masa kwatancen gidan da ya afka wa marigayin. A wannan lokacin an lura cewa yana cikin yanayi ne na maye
Ma’aikacin jinya Usman Abubakar ya tabbatar an kai Abubakar Ibrahim inda aka sanya masa magani a raunukan da ya yi, kuma aka ba shi wasu magungunan da zai sha.
Malam Ayuba Hassan Talle, Mai unguwar Limawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya kwatanta marigayin da mutum ne kamili da babu ruwansa da hayaniya da kowa, don kuwa ya dade yana zaune a unguwar.
Ya nuna takaicinsa ganin cewa al’amarin tsaro yana kara tabarbarewa, amma ya ce za su dauki matakan da suka dace domin hana aukuwar irin wannan badakalar, kuma za a yi duk abin da ya kamata domin ganin an kama Mai Kalos an mika wa hukuma.
Jami’an ’yan sanda da ke ofishin shiyya da na kula da manyan laifuffuka sun dukufa wajen zurfafa bincike da tara bayanan da suka kamata domin kama Mai Kalos don gurfanar da su a gaban kuliya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Neja, ASP Oguche Richard Adamu, ya jaddadawa wakilinmu cewar ana kan bincike game da lamarin.