Matashi ya kashe mahaifinsa a Uyo

Wani matashi mai suna Mfreke Effiong, dan kimanin shekara 25 da haihuwa ya kashe mahaifinsa mai suna Archibong Effiong.Wannan lamari, kamar yadda Aminiya ta samu labari, ya faru ne a kauyen Ikot Akpainyang Asutan, yankin karamar Hukumar Ibesikpo/Asutan, Jihar Akwa Ibom. Matashin, kamar yadda wakilinmu ya kalato, ya iske ana yin cacar baki ce tsakanin […]

Matashi ya kashe mahaifinsa a Uyo
Matashi ya kashe mahaifinsa a Uyo

Wani matashi mai suna Mfreke Effiong, dan kimanin shekara 25 da haihuwa ya kashe mahaifinsa mai suna Archibong Effiong.
Wannan lamari, kamar yadda Aminiya ta samu labari, ya faru ne a kauyen Ikot Akpainyang Asutan, yankin karamar Hukumar Ibesikpo/Asutan, Jihar Akwa Ibom.
Matashin, kamar yadda wakilinmu ya kalato, ya iske ana yin cacar baki ce tsakanin mahaifinsa da mahaifiyarsa,  shi kuma maimakon ya yi kokarin raba su ta cikin sasanci da lumana, sai ya dauko wani fallen katako ya gwabje babansa a aka; inda nan take ya fadi kasa matacce.
Wakilinmu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, domin karin haske game da lamarin. Ya ce tabbas wanda ake zargi da aikata laifi yana hannunsu suna bincikensa, da zarar sun gama bincike kamar yadda dokar kasa ta yi tanadi, za su mika shi kotu. To, ko wane dalili mai laifin ya fada wa ’yan sanda da ya sanya shi aikata haka? Jami’in dan sandan ya ce:
“Ya tabbatar mana cewa bayan da ya dawo daga gona ce sai ya iske ana cacar baki tsakanin babansa da innarsa, shi kuma da ya tambayi abin da ke faruwa aka yi masa bayani; sai ya ce baban nasa ne ke da laifi; domin a yadda ya ce mana, da baban ya gane cewa yaron ya shigo gidan sai ya dauko kwalba ya fasa don ya kore shi.
Shi kuma ganin cewa uban bai san cinsa ba bare ma shansa, shi ya sanya ya yanke wa kansa hukuncin da ya jefa shi yin nadama a yanzu.”