Matashi ya kashe mahaifinsa da wuƙa a Legas
Matashin ya daɓa wa mahaifinsa wuƙa da ƙarfe 10:00 na dare a ranar Alhamis, 3 ga Oktoba.
Wani matashi ɗan shekara 25 mai suna Chibunnma Chimelie ya kashe mahaifinsa mai shekara 68 a yankin Isolo na jihar Legas.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 4 ga Oktoba, 2024.
- Dalilin da ’yan Nijeriya za su nemi sauyin shugabanci a 2027 — Kwankwaso
- Gwamna Sule ya ’yantar da fursunoni 12 a Nasarawa
Hundeyin ya ce, matashin ya daɓa wa mahaifinsa wuƙa da ƙarfe 10:00 na dare a ranar Alhamis, 3 ga Oktoba.
Ya ce, ɗan uwan wanda ake zargin ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Aswani.
Ya ce: “Mai ƙarar ya ce maƙwabcin mahaifinsa ne ya kira shi ta wayar tarho cewa mahaifinsa ya samu rashin fahimta da wanda ake zargin, wanda ke zaune da mahaifinsa a gida ɗaya.
“Ya garzaya zuwa gidan mahaifinsa, inda ya haɗu da gawarsa marar rai a cikin jini.”
Kakakin ya ce jami’an ‘yan sanda sun ziyarci inda lamarin ya faru tare da cafke wanda ake zargin.
Ya ƙara da cewa: “Tawagar masu bincike sun ziyarci wurin da lamarin ya faru inda suka gano wata wuƙa mai ɗauke da alamar jini a kusa da gawar.
“An ɗauki hotuna sannan an garzaya da wanda aka kashe zuwa babban asibitin Isolo, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Hundeyin ya bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano al’amuran da suka faru.