Matashi ya kashe mahaifinsa saboda ya ki yi masa aure

Wani matashi mai son yin aure, mai matsakaicin shekaru, mai suna Baba Sule ya yi wa mahaifinsa mai suna Alhaji Sule Marwa kisan gilla, sakamakon kin yi masa aure, inda aka yi jinkiri, saboda wasu dalilai. Wannan lamari ya faru a garin Maisamari da ke Gembu jihar Taraba. Lamarin kamar yadda Malama Aishatu Ayuba ta […]

Matashi ya kashe mahaifinsa saboda ya ki yi masa aure
Matashi ya kashe mahaifinsa saboda ya ki yi masa aure

Wani matashi mai son yin aure, mai matsakaicin shekaru, mai suna Baba Sule ya yi wa mahaifinsa mai suna Alhaji Sule Marwa kisan gilla, sakamakon kin yi masa aure, inda aka yi jinkiri, saboda wasu dalilai. Wannan lamari ya faru a garin Maisamari da ke Gembu jihar Taraba.

Lamarin kamar yadda Malama Aishatu Ayuba ta shaida wa Aminiya, a Kalaba shi ne dan wato Baba ya na so ubansa ya yi masa aure duk da kasancewa ya sanar wa mahaifin nasa bukatar sa, amma ya yi biris da ita, abin da shi kuma Baba ya yi dukkan kokarin ganin ya shawo kan mahaifin sa ya yi masa aure tunda yakai munzali.
Jinkirin da aka samu ne na ubansa ya amsa waccan bukata tasa, ta sanya ya harzuka ya hau dokin zuciya ya dauki makami ya sara uban sa Alhaji Sule, wanda sanadiyyar hakan ya hadu da ajalinsa bayan ya yi amfani da adda ya Sassari uban nasa.
Wata majiya kusa da iyalan mamacin ta tabbatar da cewa yaron bacin rai na ganin ga budurwar sa da suke soyayya har takai jallin za su yi aure yake jiran sahalewar ubansa, abin yaci tura, ya sanya ya aikata abin da ya jefa shi tsundum cikin kogin nadama.
Yanzu dai Baba Sule zakara ya ba shi sa’a, ba a san inda ya sabe ba. Jami’an ’yan sanda sun baza komarsu, tare da shan alwashin duk inda ya shiga sai sun cafko shi.