Matashi ya kashe mahaifinsa ya kona gidansu
Litinin wannan mako ce wani matashi mai suna Onyekachi Ugwu, ya kashe mahaifinsa tare da wasu mutum takwas,wannan lamari ya faru a kauyen Ngelefi, da ke karamar Hukumar Isi-Uzo Jihar Enugu, inda iyaye da ’yan uwan makashin suke .Bayanan da Aminiya ta samu an ce wanda ake zargin sa ya dauki adda ya fafuri iyayensa, […]
Litinin wannan mako ce wani matashi mai suna Onyekachi Ugwu, ya kashe mahaifinsa tare da wasu mutum takwas,wannan lamari ya faru a kauyen Ngelefi, da ke karamar Hukumar Isi-Uzo Jihar Enugu, inda iyaye da ’yan uwan makashin suke .Bayanan da Aminiya ta samu an ce wanda ake zargin sa ya dauki adda ya fafuri iyayensa, suka gudu daga bisani tsautsayi ya fada kan mahaifinsa, inda ya yi masa mummunan sara da adda sakamakon rauni da saransa da dan ya yi ya ce ga garin ku nan . Mahaifiyarsa kuwa ta sha da kyar.
Matashin Onyekachi bai hakuraba, bayan ya kashe ubansa, ya sake dawowa ya cinna wa gidansu wuta, gobara ta kama sanadiyyar haka suka tafka asarar dabbobi da wasu daga cikin kaddarorin su. Matashin bai tsaya gidan su kadai ba, ya fito ya bazama zuwa makwabta, inda ya fada wani gida ya kashe wasu mutum tsakwas da wani karamin yaro mai shekara daya da rabi da haihuwa. Bayan matashin ya gama barnar ya gudu .
Jami’in hulda da jama,a na rundunar ’yan sandan Jihar Enugu DSP. Ebere Amaraizu ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce sun baza jami’an su domin kamo mai laifin. Halin da ake ciki inji jam’in ’yan sandan ya ce rundunar su za ta ci gaba da binciken kisan kan da aka yi.