Matashi ya kashe sama da Naira miliyan 10 wajen gyaran fuska don ko yi da Michael Jackson

Wani matashi mai suna Leo Blanco, mai shekara 22 daga babban birnin Buenos Aires, a kasar  Argentina, rahotanni na bayyana cewa matashin ya kashe sama da kudi Dala dubu $30 daidai da Naira miliyan 10,870,746.82 a cikin shekara bakwai don kawai ya kwaikwayi siffar shahararren mawakin nan Michael Jackson. Leo na daya daga cikin dubban […]

Matashi ya kashe sama da Naira miliyan 10 wajen gyaran fuska don ko yi da Michael Jackson

Wani matashi mai suna Leo Blanco, mai shekara 22 daga babban birnin Buenos Aires, a kasar  Argentina, rahotanni na bayyana cewa matashin ya kashe sama da kudi Dala dubu $30 daidai da Naira miliyan 10,870,746.82 a cikin shekara bakwai don kawai ya kwaikwayi siffar shahararren mawakin nan Michael Jackson.

Leo na daya daga cikin dubban masu kokarin kwaikwayon Michael Jackson a duniya, amma abin da ya banbanta asalin Michael Jackson da sauran masu son shiga irin na shi, shi ne ya kasance tamkar wanda masoyansa zasu bauta masa.

Leo ya fara kallon bidiyon mawakin da aka fi sani da suna sarki a bangaren da yake waka wato `King of Pop` tun yana karamin yaro kuma yana son ya zama kamar shahararren mawakin. A lokacin da yake shekara 15 Leo ya je an yi masa tiyatar roba don cimma burinsa na kama da wanda yake kauna, a cikin shekara bakwai an yi masa tiyatar sauya kamanninsa har sau 11, amma duk da haka bai gamsu da kamanninsa ba, shirinsa shi ne a sake yi masa wata tiyatar da zai zama tamkar Michael Jackson.

A wata tattaunawa da gidan talabijin Barcroft TB ya yi da Leo, ya bayyana cewa ya kashe sama da Naira miliyan 10 wajen yi masa tiyatar roba da sayan wasu kayan shafe-shafe na kwalliya. Ya ce, an yi masa tiyata har sau hudu a hancinsa da kashin kuncinsa da mukamukinsa habarsa. Wasu daga cikin masoyan Leo sun yaba da sakamakon tiyatar da aka yi masa musamman idan yana wuce wa a titunan garinsu, amma a bangaren iyalansa abin na yi masu ciwo.

Mahaifiyar Leo Blanco ako da yaushe tana cikin damuwa saboda yanayin yadda danta ya canza halittarsa, wani lokacin idan ta kalli danta sai ta ce, wannan Leo kenan? Da na kenan?

Idan aka duba tsofaffin hotunan Leo lokacin da yake karami, za a tabbatar da cewa, wadannan kayan shafe-shafen sun yi tasiri a fuskar Leo, sai dai har yanzu Leo ya ce, bai gamsku da siffarsa ba, har sai kai matsayin da ya fi kowan ne mutum me kwaikwayon  Michael Jackson kamanni a duniya.

Leo ya kara da cewa, na sadaukar da jikina da rayuwata da duk kudin da na mallaka akan in zama shahararren wanda ya fi son ya kwaikwayi Michael Jackson a duniya.

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo

China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas