Matashi ya kone gidan iyayen budurwarsa saboda yaudara

Wani matashi mai shekaru 24, Musa Abdullahi, ya banka wa gidan iyayen budurwarsa wuta saboda zargin ta yaudare shi. Tuni dai matashin da ke zaune a Unguwar Riga Fada ta Karamar Hukumar Kumbutso a Jihar Kano, ya gurfana a gaban wata kotun majistare kan wannan lamari da ake zargin ya aikata saboda budurwarsa ta koma […]

Matashi ya kone gidan iyayen budurwarsa saboda yaudara

Wasu ‘yan sandan Nijeriya

Wani matashi mai shekaru 24, Musa Abdullahi, ya banka wa gidan iyayen budurwarsa wuta saboda zargin ta yaudare shi.

Tuni dai matashin da ke zaune a Unguwar Riga Fada ta Karamar Hukumar Kumbutso a Jihar Kano, ya gurfana a gaban wata kotun majistare kan wannan lamari da ake zargin ya aikata saboda budurwarsa ta koma soyayya da wani mashinshininta.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, an gurfanar da matashin a gaban kotun wadda Rabu Abdulkadir ta jagoranta, inda ake tuhume shi da laifin yunkurin kisa da tayar da zaune tsaye.

Ana tuhumar matashin da cinna wuta a gidan iyayen tsohuwar budurwar tasa, wadda ta yi wancakali da soyayyarsa ta koma wurin wani bayan ta sa ya kamu da kaunar ta.

Bayanai sun ce budurwar wadda aka sakaya sunanta ta samu raunuka a wasu sassan jikinta sanadiyyar wutar da masoyin nata ya cinna a gidansu.

Duk da cewa lauyan masu kara ya karanta kunshin laifin kan wanda ake tuhuma, sai dai matashin ya musanta zargin.

A halin yanzu kotun ta bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan Dan Kanse har zuwa ranar 1 ga watan Yunin 2023 domin ci gaba da sauraron karar.

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba