Matashi ya mutu a artabu da ’yan sintiri
A ranar Lahadin makon jiya ne wani matashi mai kimanin shekara 27 mazaunin Unguwar Kurna a karamar Hukumar Dala ya rasa ransa sakamakon rikici a tsakaninsa da wani jami’in sintiri da ke aiki a unguwar. Rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne lokacin da ’yan sintirin suka yi kokarin kama matashin mai suna Yusuf […]
A ranar Lahadin makon jiya ne wani matashi mai kimanin shekara 27 mazaunin Unguwar Kurna a karamar Hukumar Dala ya rasa ransa sakamakon rikici a tsakaninsa da wani jami’in sintiri da ke aiki a unguwar.
Rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne lokacin da ’yan sintirin suka yi kokarin kama matashin mai suna Yusuf Mohammed da aka sani da shaye-shayen miyagun kwayoyi, inda matashin ya yi amfani da wuka ya daba wa wani dan sintirin a duwawu.
Majiyarmu ta ce, dan sintirin ya tafi ofishinsu ya sanar da abokan aikinsa halin da ake ciki, inda mutum uku suka koma wurin matashin suka yi artabu suka yi masa duka kafin su tafi da shi ofishinsu.
Aminiya ta jiyo cewa lokacin da suka isa da Yusuf ofishinsu ya gama galabaita inda daga bisani rai ya yi halinsa.
Kakakin ’Yan sandan Kano, ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce a yanzu haka ’yan sintirin hudu suna hannun ’yan sanda ana gudanar da bincike, kuma da zarar an kammala binciken kuma aka same su da laifi za a gurfanar da su a gaban shari’a, duk da cewa matashin ya yi kaurin suna a harkar daba a unguwar, inda ’yan sanda ke nemansa tuntuni.
Ya ce sun tura gawar Yusuf zuwa Asibitin Malam Aminu Kano don gano musababbin mutuwarsa.