Matashi ya mutu a tafki yana wanka a Kano
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce, wani matashi mai kimanin shekara 20, mai suna Mustapha Abdullahi, ya nutse lokacin da yake wanka a wani tafki da ke Kofar Mata a yankin Hauran Balago cikin birnin Kano. Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobarar jihar Kano Saidu Mohammed, ne ya sanar da hakan […]
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce, wani matashi mai kimanin shekara 20, mai suna Mustapha Abdullahi, ya nutse lokacin da yake wanka a wani tafki da ke Kofar Mata a yankin Hauran Balago cikin birnin Kano. Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobarar jihar Kano Saidu Mohammed, ne ya sanar da hakan a yau lokacin da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin labarai NAN.
Saidu, ya ce Mustapha ya nutse ne a safiyar yau Juma’a lokacin da ya shiga tafkin yana wanka. Hukumar ta samu rahoton nutsewar Mustapha ne lokacin wani mai suna Malam Muhammadu Rabiu, ya kira ofishin hukumar da misalin karfe 8:00 na safe yana watangaririya a saman ruwa.
Bayan kai Mustapha asibiti an tabbatar da ya rasu a cikin ruwan.