Matashi ya mutu ana cikin tafiya a motar haya

Dan shekara 29 ya yanke jiki a fadi a mace suna tsaka da tafiya a motar haya

Matashi ya mutu ana cikin tafiya a motar haya

Wani matashi dan shekara 29 ya yanke jiki a fadi a mace a lokacin da suke tsaka da tafiya a cikin motar haya a Jihar Ogun.

Matashin mai suna Anuoluwapo Aderemi, ya rasu a cikin bas din ne cikin dare, a lokacin da suka tsaya shan mai a wani gidan mai a yankin Itori.

Rundunar ’yan sanda da ke Jihar Ogun ta ce ya rasu ne hanyarsu ta zuwa Ibadan,  babban birnin jihar Oyo, daga Papalanto a Karamar Hukumar Ewekoro.

Kakakin rundunar, Odutola Omolola, ta ce direban motar ne ya sanar da su game da rasuwar matashin a cikin bas dinsa mai dauke da fasinjoji daga Papalanto.

“A lokacin da direban yake shan mai da misalin karfe 7:00 na dare ne fasinjoji suka sanar da shi cewa matashin ya fita daga hayyacinsa daga karshe rai ya yi halinsa.

“An kai gawar asibitin da ke Ifo inda likita ya tabbatar da rasuwar,” in ji ta.

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato