Matashi ya rasu a gidan budurwarsa a Kano

“Akwai rauni a kansa, kuma muna zargin an doka masa wani abu ne,” in ji abokin mamacin.

Matashi ya rasu a gidan budurwarsa a Kano

Wani matashin ɗan kasuwa ya rasu a gidan wata fitacciyar ’yar TikTok da aka fi sani da Fati Cele, wadda budurwarsa ce da ke zaune a unguwar Danbare da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

Rahotanni sun ce matashin mai suna Isma’il Makaye, wanda ke sayar da kayan kwalliya a unguwar Hotoro Tishanma, ya rasu ne da safiyar ranar Juma’a, amma tuni ’yan sanda suka fara bincike.

Wani abokin mamacin, Hassan Mohammed, wanda yana cikin mutanen da suka je wajen da lamarin ya faru tare da ’yan sanda, ya shaida wa Aminiya cewa lokacin da suka isa, Makaye ya rasu.

A cewarsa, daga baya aka kai gawar zuwa Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad, sannan aka tura su zuwa Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase, inda aka tabbatar da rasuwarsa.

“Mun tarar da shi ya riga ya rasu lokacin da muka isa tare da ’yan sanda. Da farko mun je asibitin Murtala, daga baya kuma aka tura mu Asibitin Nassarawa, inda aka tabbatar da mutuwarsa,” in ji Hassan.

Ya kuma bayyana cewa Makaye da Fati Cele sun shafe sama da da shekara biyu suna soyayya, amma sun rabu bayan da mamacin ya yi aure, kafin daga bisani suka sake shiryawa.

Hassan ya yi zargin cewa akwai saɓani tsakanin mamacin da budurwar a ranar da abin ya faru, bayan da Fati Cele ta zargi Makaye na shirin zuwa wajen wata budurwa.

A cewarsa, an tarar da wayoyin mamacin guda biyu da kuma makullin motarsa a gidan.

A cewar abokin, an ga rauni a kan mamacin wanda ake zargin an buga masa wani abu, inda ya ce har lokacin da aka yi jana’izarsa jini na zuba.

“Akwai rauni a kansa, kuma muna zargin an doka masa wani abu ne,” in ji abokin mamacin.

An yi jana’izar Makaye a ranar Juma’a a Unguwa Uku ’Yan Awaki bisa tsarin addinin Musulunci.

Lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, musamman TikTok, inda mutane ke kira da a gudanar da bincike kan musabbabin mutuwarsa.

Fati Cele, wadda ’yar asalin Jihar Borno ce, tana rawar Gala a Sabon Gari da ke Kano.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba domin jin ta bakinsa kan lamarin ba.