Matashi ya rataye kansa a Kaduna

A ranar Litinin da ta gabata ce a Unguwar Mando da ke Kaduna aka iske gawar wani matashi a rataye a bishiyar mangwaro. Matashin mai kimanin shekara 20 mai suna Abel Fada an sinci gawarsa ne rataye a gefen titin da ake kira Bush Close a kusa da ofishin kamfanin lantarki na Mando. daruruwan mutane […]

Matashi ya rataye kansa a Kaduna
Matashi ya rataye kansa a Kaduna

A ranar Litinin da ta gabata ce a Unguwar Mando da ke Kaduna aka iske gawar wani matashi a rataye a bishiyar mangwaro.


Matashin mai kimanin shekara 20 mai suna Abel Fada an sinci gawarsa ne rataye a gefen titin da ake kira Bush Close a kusa da ofishin kamfanin lantarki na Mando.

daruruwan mutane sun yi ta tururuwa zuwa wurin domin cire kwarkwatar ido duk da warin da aka ce gawar ta fara yi, wadda ga alama babu wanda ya san kwanakin da ta yi a rataye saboda mutane ba su cika bi ta hanyar ba.
Kawunsa Dominic Apolo, ya ce tun ranar Juma’ar makon jiya suke neman matashin. “dan babban yayana ne, kuma mahaifansa duka sun mutu. A kullum yakan fada min cewa ba ya iya barci ni kuma na sha tambayarsa dalilin da ya sa ba ya iya barci. Nakan tambaye shi ko yana cikin kungiyar matsafa ce ko yana da wata matsala ce, ya fada min domin in magance masa ita amma sai ya ce babu matsala,” inji shi.
Ya ce, “Kwanan nan ya kammala karatunsa na sakandare har ya fara zuwa makarantar koyon kwamfuta. Amma a makon jiya ya fada min cewa ba ya jin dadi, nan take na sa aka kula da shi bayan ya samu sauki sai ya ce da ni zai ci gaba da karatunsa na kwanfuta. Tun daga ranar muke ta nemansa ba mu gan shi ba, da ba mu gan shi ba sai muka zata ya koma gida Jihar Edo ne, tunda kanwata da ke kula da shi, ta ba shi kudi a ranar Juma’a kafin ta wuce Abuja.”
Ya ce bayan kanwarsa ta dawo daga Abuja ne sai ta tarar duk kofofin gidan a kulle da taga haka sai ta kira lambar wuyarsa amma ba a dauka ba. Shi ne ta kira wani kafinta ya balle kofar kafin a sanar da ’yan sanda.  
Wani jami’in ’yan sanda a ofishinsu na Mando da bai son a ambaci sunansa ya tabbatar da cewa iyalan marigayin sun sanar da bacewar Abel ga ofishin. Ya ce a ranar Litinin da ya samu labarin an ga gawar wani da ya rataye kansa a bishiya, “sai na bukaci a kai ni wurin da na dubi hoton da iyayensa suka ba mu, sai na ga shi ne, daga nan ne na kira ’yan uwansa inda suka tabbatar da cewa shi ne,” inji shi.  
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Aminu Lawan ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce tuni rundunar ta fara bincike domin gano abin da ya sa ya halaka kansa.