Matashi ya sace N120m a asusun makwabcinsa

An kwace kudi miliyan N35 da gine-gine da manyan shaguna da sauran kadarori a hannun matashin

Matashi ya sace N120m a asusun makwabcinsa

’Yan sanda sun kama wani matashi mai shekaru 34 kan zargin damfarar wani makwabcinsa a kasuwa Naira miliyan 120 a Jihar Bauchi.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil, a cikin wata sanarwa, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan  “Koken da mai kudin ya kai wa  gaban ’yan sanda cewa an cire kudi Naira miliyan biyu da dubu sittin da takwas daga asusun bankin kamfaninsa.”

Wakil ya ce, “sakamakon haka kwamishinan ’yan sandan jihar, Auwal Musa Mohammed, ya bada umurni a yi bincike a kan lamarin ba tare da bata lokaci ba.

“Binciken ya gano cewa wanda ake zargin ya cire Naira miliyan 120 a asusun bankin mai karar ba bisa ka’ida ba a lokuta daban-daban.

“A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amince cewa ya ci amanar makwabcinn nasa, wanda suka yi tarayya da shi a kasuwa na sama da shekaru 15.

“Wanda ake zargin ya bayyana cewa wani abokinsa da suka hadu a kwalejin kimiyya da koyon sana’oi na tarayya da ke Bauchi, wanda ya samu horo da aiki a fannin ilimin kwamfuta ne ya sa shi yin damfarar.

“Ya ce abokin nasa ya tabbatar masa cewa zai iya samun kudi ta hanyar shiga wayar wani mai hannu da shuni, ya ci bashi a waya, inda ya baiwa abokin aikinsa damar shigar kudi zuwa asusun bankuna daban-daban a lokuta daban-daban.”

Wakil ya ce, “Abuwanan da aka kwato a hannun matashin da ake zargin sun hada da tsabar kudi miliyan N35, manyan shagunan dinkin kaya na zamani guda biyu, gine-gine biyu da ba a kammala ba, Keke Napep guda takwas, buhu 60 na gawayin girki, takin zamani buhu 30 da babura biyu.”

Ya ce, “Wanda ake zargin, ya tabbatar wa kawunsa da budurwarsa cewa yana samun kudi ne ta hanyar kasuwanci ta intanet, lokacin da suka tambaye shi hanyar da yake samun kudi.”

Jami’in ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, sannan ya bukaci jama’a da su sanya ido tare da tabbatar da tsaron kudadensu tare da kai rahoton ga ’yan sanda ko a kira.

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya

Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka

Tags