Matashi ya shiga hannu kan sace yaro ɗan shekara 2 a Kano

Matashin ya ɓoye yaron a wani gida da ke unguwar Dorayi, sannan ya nemi miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa.

Matashi ya shiga hannu kan sace yaro ɗan shekara 2 a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, sun kama wani matashi mai shekaru 25, kan zargin sace wani yaro ɗan shekara biyu a duniya, Al’amin Ahmad Garba, tare da neman kuɗin fansa Naira miliyan 50.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 25 ga watan Disamban 2024.

An gano yaron a wani gida da ke unguwar Dorayi bayan ya shafe kwanaki uku a ɓoye.

Bayan an ceto yaron, an kai shi Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad don duba lafiyarsa, sannan aka miƙa shi ga iyayensa.

An gurfanar da wanda ake zargin a kotun majistare mai lamba 25 da ke Nomansland, a Kano.

Kakakin ya ce matashin yanzu haka yana tsare a hannun hukuma, yayin da ake ci gaba da shari’a.

Tsofaffin ma’aikatan Gombe 2,204 sun karɓi giratuti N4.2bn

Bam ya yi ajalin ɗaliban Islamiyya 2 a Abuja 

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Saudiyya

’Yan sanda sun ceto yara 4 da aka sace daga Bauchi a Anambra