Matashi ya tara ’yar tsana sama da dubu shida a kan Naira miliyan 61
Mista Jian Yang, wani matashi dan kasar Singafo, mai shekara 33 ya dukufa wajen tara ’yar tsana, inda a halin yanzu ya mallaki diyar bebi sama da dubu shida iri daban-daban. Ya yi dangin na’ukan ’yar tsanarsa sama da dubu shida a kawataccen dakin hutawarsa. kimar kudin ’yar tsanarsa ya fi Naira miliyan 61.“Ni mutum […]
Mista Jian Yang, wani matashi dan kasar Singafo, mai shekara 33 ya dukufa wajen tara ’yar tsana, inda a halin yanzu ya mallaki diyar bebi sama da dubu shida iri daban-daban. Ya yi dangin na’ukan ’yar tsanarsa sama da dubu shida a kawataccen dakin hutawarsa. kimar kudin ’yar tsanarsa ya fi Naira miliyan 61.
“Ni mutum ne wanda ba shi da tsari,” a cewar Mista Yang, kamar yadda ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters. “Idan ka hadu da ni a wajen idan nan, za ka ga na sha bamban da yadda ka ganni a yanzu. Don ban yi kama da mai tara ’yar tsana ba,” inji shi.
Mista Yanga ya darsu da soyayyar ’yar tsana tun yana dan shekara 13, inda ya sayi wata ’yar tsana mai siffar manyan ’yan kwalisa (Great models), a wani wurin motsa jiki na “turkuoise Spanded gym.” Kafin in san wani al’amari game da zamantakewar al’umma, ni yaro ne mai sha’awar kallon talabijin, a lokacin na fara sha’awar diyar bebi, amma ba ni da ikon mallakar daya, a cewarsa. “Dan a fara girma, ina dan samu kudin kashewa, sai na fara samun ’yancin sayen abin da nike so,” inji shi.
Wannan sha’awa ta kuruciya ta “tsananta kamar hauka” har ya samu goyon baya daga abokai, kuma iyaye da ’yan uwa suka hakura da shi a a haka. A cewar Mista Yang, “na himmatu wajen tara kayayyaki, kuma ’yan matana duk sun rabu da ni saboda bas a jin dadin wannan dabi’a. Da sun kalli tarin ’yar tsana sai su tafi abinsu, wato suna gasa (kishi) da su, al’amarin dai akwai tashin hankali, amma gaskiya ce ta hakika,” inji shi.
Wannan matashi mai tsananin son ’yar tsana, ya yi ikirarin kashe akalla Dala dubu 392, cikin shekara 20, wajen sayen nau’ukan ’yar tsana, wadanda suka hada da diyar bebi ta Bratz Girls da Monstwer High and Jem da holograms lines. Mista Yang ya ce diyar bebi na da makoma, wato kimar darajarta za ta daga a gaba.
“A hanyata ta zuwa wajen aiki, ko tafiye-tafiyena, a nan nake samun diyar bebi,” inji Yang
A tafiyar da ya yi zuwa birnin New York ta Amurka, ya sayo ’yar tsana har 65. Kuma yana shirin komawa a wannan watan, yana da tabbacin a wannan karon ma zai ziyarci kantuna. Yang dai yana smaun kyautar ‘’yar tsana da diyar bebi, sannan yana sayensu a wurin gwanjo, ko kuma ta shafukan kasuwanci a yanar sadarwar intanet.
Al’amarinsa sai gaba-gaba yake yi, don haka aka bijiro masa da tambaya kan cewa, idan wurinsa ya cika ya ya zai yi? Sai ya amsa da cewa “zan sayi wancan gida,” yana dariya ya nuna gidan d ake kusa d anasa. “Kuma har yanzu ina da filin da bai cika ba,” inji shi.