Matashi ya yi garkuwa da kansa don karbar N10m daga iyayensa

An kama shi tare da wata budurwa da wasu abokan cin mushensu guda uku a Jihar Ogun.

Matashi ya yi garkuwa da kansa don karbar N10m daga iyayensa

Jami’an ‘Yan sanda

Aisirin wani matashi ya tonu bayan ya yi garkuwa da kansa domin tatsar iyayensa Naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa.

An kama matashin mai shekara 23 tare da wata budurwa da wasu abokan cin mushensu guda uku a Jihar Ogun.

Kakakin ’yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce dubun matasan ta cika ne bayan yayan matashin ya kai rahoto cewa masu ’yan bindiga sun yi garkuwa da kaninsa a hanyarsa ta zuwa Legas daga Kalaba, kuma suna neman kudin fansa Naira miliyan 10.

Bayan kai rahoton a Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Mowe a garin Abekuta, hedikwatar jihar ne DPO na yankin, SP Folake Afeniforo, ya tura jami’ansa zuwa wurin.

Oyeyemi ya ce bayan isar jami’ansu wurin sun samu matashin a cikin wani kango, an daure hannuwansa da kafafunsa, tare da wasau mutum biyu ciki har wa wani dan kasar Ghana.

Nan take aka cafke sauran mutanen, shi kuma aka kubutar da shi, “Amma da aka kawo wadanda ake zargin ofishin ’yan sandan sai suka fallasa cewa shi ne ya kitsa garkuwar da shi domin ya tatsi iyayensa kudi, zai fara kasuwanci ta intanet.

“Budurwar da wani wanda suka fito tare daga Karamar Hukumar Yala ta Jihar Kuros Riba ne suka hada su da wadanda aka fara kamawa kuma dukkansu ne suka hada baki wajen garkuwa da shi.

“Bayanan da suka bayar sun taimaka wajen kamo budurwar da daya saurayin kuma su ma sun amsa abin da ake zargin su da aikatawa, in ji Oyeyemi.

Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, Lanre Bankole, ya umarci sashen yaki da masu garkuwa da mutane na Babban Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunan ya zurfafa bincike kan lamarin kafin gurfanar da matasan a kotu.