Matashi ya yi kwana 4 da harbin harsashi a cikin kokon kansa

Matashin ya yi tunanin an same shi da dutse ne a jajibirin sabuwar shekara.

Matashi ya yi kwana 4 da harbin harsashi a cikin kokon kansa

Mateus Facio kwance a gadon asibiti bayan an yi masa tiyata

Wani dan kasar Brazil mai suna Mateus Facio zai iya daukar kansa a matsayin mai sa’a da ya rayu bayan da aka harbe shi da bindiga a kai saboda ya yi tunanin an same shi da dutse ne a jajibirin sabuwar shekara kuma a haka ya ci gaba da gudanar da harkokinsa na tsawon kwana hudu.

Mateus Facio mai shekara 21 a duniya yana cikin liyafa a gabar kogin Cabo Frio a cikin Jihar Rio de Janeiro a ranar 31 ga Disamban da ya gabata, sai ya ji kara mai karfi, kamar fashewa a kansa, sannan ya biyo baya da zafi mai tsanani.

Sai ya dora hannunsa a saman kansa ya ga jini.

Wani likita a cikin taron ya lura da jinin da ke kwararowa daga kansa kuma ya taimaka wajen dakatar da zuban jini, amma yana tunanin cewa kawai wani dutse ne aka jefe shi da cikin zafin rana, Mateus ya ci gaba da harkokinsa.

Sai kawai ya shafa kankara a kan raunin, ya yi bikin Sabuwar Shekara tare da abokai, sannan ya yi tuki mai nisan kilomita 300 zuwa gidansa a garin Juiz de Fora.

A ranar 3 ga Janairu, ya tafi aiki kamar yadda ya saba.

Sannan ya wuce Rio de Janeiro don haduwa da wasu abokai, kuma sai da yamma a ranar 4 ga Janairu ya fahimci akwai wani abu ba daidai ba.

Bayan ya yi barci kadan a ranar 4 ga Janairu, Mateus ya ji hannunsa na hagu ya yi nauyi fiye da yadda ya saba.

Zai iya motsa shi, amma yana jin sabon abu, kamar ba ya da ikon daukar wani abu da shi.

Cike da damuwa ya sa kaya ya nufi wani asibiti mai zaman kansa kai-tsaye, inda ya shaida wa likitoci abin da yake tunani game da dutsen da aka jefe shi da shi a kai kwana hudu da suka wuce.

Sai dai da aka sa na’urar daukar hoton sassan jiki sai ta nuna cewa ba dutse ba ne harsashi ne a cikin kokon kansa.

“Likitoci da ma’aikatan jinya da suka ga Mateus a wurin kusan ba za su yarda ba,” wata mahaifiyar daliba, mai suna Luciana, ta bayyana wa tashar Talabijin ta Globo.

“Domin mutum ya kwana hudu da harsashi a kai, ba tare da ya ji wani abu da ba zai iya bayyanuwa ba,” in ji ta.

Likitoci sun bayyana wa Mateus da iyalansa cewa dole ne a cire harsashin da ke cikin kwakwalwarsa mai girma milimita 9 ta hanyar tiyata.

Kuma duk da cewa yana cikin wani bangare marar hadari na kwakwalwarsa, zai iya haifar da babbar matsala a nan gaba.

Kamar hadarin kamar zubar jini a kwakwalwa, har ma da mutuwa. Kuma aikin ya yi nasara, Mateus ya riga ya fara cikakkiyar farfadowa.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja