Matashi ya yi wa abokinsa yankan rago kan N750
Wani matashi mai suna Stephen Onuoha ya yiwa abokinshi Daniel Bassey yankan rago yai kuma gunduwa-gunduwa dashi saboda ya kasa biyarshi N750 da yake binshi har tsahon shekaru biyu. Onuoha dan shekara 32 da haihuwa dan asalin jahar Anambra ne amma yana zaune a jahar Akwa Ibom shikuwa abokin nasa Daniel Bassey wanda yake sana’ar […]
Wani matashi mai suna Stephen Onuoha ya yiwa abokinshi Daniel Bassey yankan rago yai kuma gunduwa-gunduwa dashi saboda ya kasa biyarshi N750 da yake binshi har tsahon shekaru biyu.
Onuoha dan shekara 32 da haihuwa dan asalin jahar Anambra ne amma yana zaune a jahar Akwa Ibom shikuwa abokin nasa Daniel Bassey wanda yake sana’ar wanzanci dan asalin jahar Akwa ibom daga karamar hukumar Uruan.
Aminiya ta samu damar zantawa da wanda ake zargi inda ya bayyana mata cewa “Gayyatarsa nayi dakina nace masa yazo zamu gana matsayin mu na abokai zamu tattauan wasu matsaloli na rayuwa shine bai yi kasa a gwiwa ba yazo gidana ni kuma kafin yazo na sanya kayan maye da zasu gusar masa da hankali cikin barasa dazan bashi yasha ni kuma insha wadda ban gurbata taba.”
Ya ce “Daga nan bayan yasha giyar sai maye ya kamashi ya bugu har takaishi da fita hayyacinsa ni kuma sai na daure hannuwansa da kafafuwansa naci gaba da sassarashi gunduwa gunduwa”.
Har wayau Stephen Onuoha yaci gaba da cewa “shekara biyu da suka wuce naba shi rancen kudi naira 750 domin yaja jari yace min shagon aski zai bude amma har yanzu shi bai nunamin abunda yayi da kudin ba bai kuma mayar min da kudina ba bai kuma tsinana komai ba duk lokacin da na tambaye shi sai ya harzikomin karshe har ‘yansandan SARS na sanar mawa suna sane da batu amma yaci tura shi yasa bakin cikin haka ya sanya na kashe shi.”
Kwamishinan ‘yan sandan jahar Gabriel Achong ya tabbatarwa Aminiya cewa wannan abu ya faru ne da misalign karfe uku na dare ne wanda ake zargin ya fara yanka abokinsa ya raba kansa daga nan kuma ya shiga rabashi gunduwa gunduwa.
“Sannna sai ya nemi katuwar jaka ya sanya ciki ya kama hanyar Itu ganin asirinsa zai tonun a nasa wayo sai ya cire wasu sassan jikin mamacin da suka hada da hannuwa da sauran nsassan jiki kuma ya boye su a wani layi Mai suna layin makaranta”
Kwamishinan ya ce sun sami nasarar cafke Stephen Onuoha, da taimakon maigidan da Onuoha yake zaune inda ya garzaya ya sanarwa da rundunar ‘yan-sanda.