Matashi ya yi wa tsohuwa ‘yar shakera 70 fyade

Wani matashi dan shekara 25 da ya yi wa tsohuwa ‘yar shekara 70 fyade ya daura alhakin laifin a kan giya. Ana zargin Wasiu Bankole da haurawa gidan wata tsohuwa a unguwar Abule Lemode da ke yankin Ijoko a jihar Ogun inda ya yi mata fyade a ranar Talata, 2 ga watan Yuli. Mai Magana […]

Matashi ya yi wa tsohuwa ‘yar shakera 70 fyade

Wani matashi dan shekara 25 da ya yi wa tsohuwa ‘yar shekara 70 fyade ya daura alhakin laifin a kan giya.

Ana zargin Wasiu Bankole da haurawa gidan wata tsohuwa a unguwar Abule Lemode da ke yankin Ijoko a jihar Ogun inda ya yi mata fyade a ranar Talata, 2 ga watan Yuli.

Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa sun kama matashin ne bayan tsohuwar mai shekaru 70 wadd aka sakaya sunanta ta shigar da karar cewa matashin ya haura gidanta ya yi mata fyade.

“Ta ce da misalin karfe 8 na dare ya haura gidan nata ya yi mata fyade da karfin tsiya.

“Ihun da ta yi ta kurmawa ne ya sa wani makwabcinta ya je da sanda domin kai mata dauki.

“Ko da ya isa sai ya iske matashin ya danne tsohuwar, sai ya buga masa sandar amma ya samu tserewa a lokacin inda ya bar rigarsa da wandonsa da fitilar hannu a dakin datijjuwar,” inji shi.

DSP Oyeyemi ya ce an kama wanda ake zargin ne cikin awa 24 da aikata laifin bayan da matar ta kai kara inda DPO yankin Kuranga Yero ya jagorancin jami’ansa suka kuma yi nasarar kame wanda ake zargin.

“A lokacin da ake bincike, matashin ya amsa laifinsa inda ya ce ya yi hakan ne a lokacin da yake cikin mayen giyar da ya sha kafin ya aikata laifin.

“Yanzu haka an garzaya da tsohuwar asibiti domin kula da lafiyarta,” inji shi.

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kenneth Ebrimson ya ba da umarnin tusa keyar matashin zuwa Sashen Bincike Manyan Laifukan Tauye Hakkin Yara da ke babban ofishin rundunar a Abeokuta Babban Birnin jihar.