Matashi ya yi wa ’yar masoyiyarsa fyade
Wani matashi da ya yi wa ’yar masoyiyarsa fyade ya shiga hannun Hukumar Sibil Difens a garin Abeokuta na JIhar Ogun
Wani matashi da ya yi wa ’yar masoyiyarsa fyade ya shiga hannun Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a garin Abeokuta na JIhar Ogun.
Matashin mai shekaru 35 ya yi wa yarinyar fyade ne alhali ya kasance yana soyayya da mahaifiyarta.
Kakakin Hukumar NSCDC na Jihar Ogun, Dyke Ogbonna, ya ce iyalan yarinyar ne suka kawo wa hukumar kara,”bayan bincike kuma wanda ake zargin ya amsa laifin, don haka za a gurfanar da shi a gaban kotu.”
Jami’in ya gargadi iyaye musamman uwaye da su hana ’ya’yansu mata cudanya da maza, saboda gudun abin da ke iya zuwa ya dawo.
- Kano: Abba ya nada Darakta-Janar kan tallace-tallace a titi
- NNPP, PDP da wasu jam’iyyu 5 sun kulla ƙawancen siyasa
Wanda ake zargin ya shaida wa manema labarai cewa yana soyayya da mahaifiyar yarinyar kafin uwar ta yi tafiya zuwa kasar Isra’ila a shekarar 2017.
Ya kara da cewa bayan ya sadu da yarinyar, ya ba ta lemon taba ta sha don kada ta dauki juna biya.