Matashi ya yi wa ’yar shekara 4 yankan rago a gidansu
Ita kanta mahafiyar yarinyar tserewa ta yi don tsira da ranta
An kama wani matashi kan yi wa ’yar makwacinsa mai shekaru hudu yankan rago a lokacin da take tsaka da barci.
Rundunar ’yan sanda Jihar Enugu ta ce matashin dan shekaru 30 yana tsare a hannunta, kuma ya amsa lafin da ake zargin sa.
Kakakin rundunar, DSP Daniel Ndukwe, ya ce, “Da wuka ya yi mata yankin rago, ita kanta mahafiyar yarinyar tserewa ta yi don tsira da ranta, sai daga baya ta dawo da kurar ta lafa.
“Wanda ake zargin ya amsa lafin, da cewa miyagun kwayoyin da ya sha ne suka sa ya fita daga hayyacinsa ya aikata hakan.”
- Mai shayi ya kashe saurayi saboda taliyar yara a Jigawa
- Ina sukar Tinubu ba don na tsane shi ba — Jigo a NNPP
- Mai kai wa ’yan ta’adda kakin sojoji ya shiga hannu a Kaduna
DSP Nwukwe ya bayyana cewa bayan samun labari ’yan sanda suka garzaya layin Orba da ke Karamar Hukumar Nsukka, “suka kai yarinyar asibiti, inda likita ya tabbatar ta rasu, kafin a mika gawar a mutuware.”
A cewarsa, an gano wukar da ake zargi matashin ya yi mafani da ita waje yi wa yarinyar yankan rago, da wasu layu da kuma kullin ganye da ake zargin tabar wiwi ne.
“Wanda ake zargin yana daga cikin mutanen da ke zaune gida guda da iyayen yarinyar.
“Binciken farko ya nuna ya sai da ya fara yunkurin kai wa wasu makwabta hari kafin ya shiga dakin da yarinyar take kwance tana barci ya yi mata yankan rago,” in ji Ndukwe.
Jami’in ya ce matashin ya shaida wa masu bincike cewa shi dan wata kungiyar asiri ne da ya shiga garin Jos, Jihar Filato, tun shekarar 2022, kuma ya taba kashe a wani dan kungiyar abokan gabansu.
Daga nan ya ce za a gurfanar a matashin a kotu idan aka kammala bincike kan lamarin, wanda kwamishinan ’yan sandan jihar Enugu, Kanayo Uzuegbu, ya bayar da umarcin a zurfafa bincike a kai.