Matashi ya yi wa ’yar yayarsa fashi da makami a Katsina

Ya ɗaure ta da igiya ya kuma rufe mata baki. Amma da ya yi zargin cewa ta daina numfashi, sai ya ja ta zuwa banɗaki, inda ya bar ta a kwance.

Matashi ya yi wa ’yar yayarsa fashi da makami a Katsina

Taswirar Jihar Katsina

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta kama wani matashi mai suna Adamu Ibrahim Tama mai kimanin shekara 20 bisa zarginsa da yi wa ’yar yayarsa fashi da makami.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar, ya ce mahaifiyar yarinyar, Fatima Nura Lawal, mai suna Hajiya Jamila Ibrahim Tama, wadda kuma ’yar uwar wanda ake zargin ce, ita ce ta kai ƙorafi a Ofishin ’Yan Sanda na Sabon Gari.

A cewarsa, Hajiya Jamila ta kai rahoton ne a ranar 22 ga Yunin 2026, inda ta zargi ɗan uwanta da kai wa ’yarta hari da niyyar yi mata fashi.

Sanarwar ta ce a ranar da lamarin ya faru, Adamu ya kai wa Fatima hari da wuƙa da kuma itacen girki, lamarin da ya janyo mata munanan raunuka a kunnen dama da wasu sassan jikinta.

Bayan haka, ya ɗaure ta da igiya ya kuma rufe mata baki. Amma da ya yi zargin cewa ta daina numfashi, sai ya ja ta zuwa banɗaki, inda ya bar ta a kwance.

Ana zargin ya kwashe wayoyin salula guda biyu — iPhone 13 Pro Max da Samsung — waɗanda aka ƙiyasta darajarsu ta kai Naira 175,000 da Naira 185,000 bi da bi, da kuma wata na’urar power bank mai darajar Naira 20,000.

Tuni dai an garzaya da Fatima zuwa asibiti, yayin da jami’an ’yan sanda suka fara bincike, wanda ya kai ga cafke Adamu Ibrahim Tama.

Rundunar ta ce an kuma ƙwato wasu kayayyaki daga hannunsa, ciki har da wata wuƙa mai ɗauke da alamun jini, wadda ake zargin ita ce ya yi amfani da ita wajen aikata laifin.

’Yan sanda sun ce da zarar sun kammala bincike, za su gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa tanadin doka.