Matashi ya yi yunkuri halaka mahaifinsa a Gombe

An gurfanar da wani matashi dan kimanin shekara 33, Muhammadu Ishiyaku a gaban kotun yanki ta daya da ke Unguwar Bolari Gombe, bisa yunkurin neman halaka mahaifinsa da wuka. Aminiya ta samu zantawa da matashin a cikin harabar kotun kafin alkali ya saurari karar da mahaifinsa ya shigar gabanta, don jin dalilin da ya sa […]

Matashi ya yi yunkuri halaka mahaifinsa a Gombe

An gurfanar da wani matashi dan kimanin shekara 33, Muhammadu Ishiyaku a gaban kotun yanki ta daya da ke Unguwar Bolari Gombe, bisa yunkurin neman halaka mahaifinsa da wuka.

Aminiya ta samu zantawa da matashin a cikin harabar kotun kafin alkali ya saurari karar da mahaifinsa ya shigar gabanta, don jin dalilin da ya sa yake neman halaka mahaifinsa ta hanyar kokawa har ya yanke shi da wuka.

Matashin ya tabbatar da cewa sun samu sabani da mahaifinsa Malam Ishiyaku amma bai nemi halaka shi ba sai dai sun yi kokawa har mahaifin nasa ya daga shi ya buga shi da kasa, ya sa aka kama shi aka kawo shi gaban alkali amma shi bai yanke shi da wuka ba.

“Yaddikona ce take mani munafunci a wajen babana, take ce masa ina satar kaji kuma ni ba barawo ba ne. Shi kuma ba ya yin bincike idan ta fada masa magana kawai sai ya hau ni da fada. Shi ne abun ya fara isa ta,” inji matashin.

Ya kara da cewa “wallahi ni ban nemi kashe mahaifina ba kuma ai ko giya nasha ba zan ce zan kashe shi ba. Kokawa muka yi da shi, a nan ne ya ji ciwo da wukar da ta

Mahaifinsa Malam Ishiyaku Dauda dan shekara 76 ya fada wa Aminiya cewa Muhammadu dansa ne amma ya fi karfinsa, domin ya nemi halaka shi saboda yana hana shi taba kayan mutane, yana so ya shiryu amma shi ya ki natsuwa sai dauke-dauken kayan mutane.

Ya kara da cewa babu irin tarbiyyar da bai shi ba, a boko ya ki karatu, hatta wuraren sana’o’i daban-daban har goma sha biyu ya kai shi yana kirgawa amma ya ki tsayawa ya koyi sana’a. Ya kai shi wajen abokansa direbobi har mutum shida daban-daban su koya masa aikin mota, nan ma ya ki sai yawon sace-sace da shaye-shayen kayan maye.

Da kotu ta tuntubi Muhammadu Ishiyaku kan zargin da mahaifinsa yake masa na neman halaka shi, ya amince da laifinsa. Daga nan sai alkali Garba Abubakar Dule ya yi amfani da sashi na 168 da kuma na 78 na kundin laifuffuka da hukunci PC ya yanke masa hukuncin zaman gidan kurkuku na tsawon watanni 60.