Matashi ya yi yunkurin hallaka kansa kan bashin N2m a Kano

Matashin ya ce bashi ya yi masa ƙatutu.

Matashi ya yi yunkurin hallaka kansa kan bashin N2m a Kano

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta ceto wani matashi mai shekara 37 da ya yi kokarin rataye kansa kan bashin miliyan biyu da ake bin sa.

Matashin mai suna Saifullah Rabiu, ya rubuta takarda game da kashe kansa, inda ya bayyana cewa ya yi hakan ne saboda bashin Naira miliyan biyu da ake bin sa.

Matashin, ya bayyana cewar ya ci bashin ne lokacin da yake neman bizar zuwa kasar waje.

Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

A cewar sanarwar, hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 10:07 na safe daga Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta jihar.

Sun shaida wa hukumar faruwar lamarin a kan titin Gidan Gwamnati kusa gidan Sarki na Nassarawa.

Hukumar ta aike da jami’anta wurin da misalin karfe 10:10 na safe.

Kakakin, ya bayyana cewar an samu Saifullahi cikin mawuyacin hali kafin ceto shi.

Matashin dai ya zayyana yadda bashi ya yi masa ƙatutu, wanda iya dubu 500 kadai ya iya biya daga abin da ake bin sa.

Kazalika, ya bayyana yadda bashi ya addabi rayuwarsa wanda daga karshe ya yanke shawarar hallaka kansa.

Tuni hukumar ta mika matashin ga jami’in kula da laifuka, Zaharaddini na sashen ‘yan sanda da ke yankin Farm Center domin ci gaba da bincike.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja