Matashi yana neman wanda zai saye shi a Kano
Ya ce shi tela ne, amma matsin rayuwa ne ya sa yake son sayar da kansa N20m.
Wani matashi mai shekara 26 ya sa kansa a kasa yana neman wanda zai saye shi a Kano.
Matashin mai suna Aliyu Na Idris, wanda dan asalin Jihar Kaduna ne, yana yawo ne a kan tituna a Kano, dauke da kwali da aka rubuta “wannan mutumin na sayarwa ne a kan Naira miliyan 20.”
Shi dai Aliyu, wanda ya shafe kimanin kwana biyar yana yawon neman wanda zai saye shi a garin Kano, ya shaida wa Aminiya cewa shi tela ne, matsin rayuwa ce ta sa yake son sayar da kansa N20m, kuma da sanin iyayensa.
Ya ce da farko sai da ya fara tallata kansa a Kaduna ko za a samu mai sayen shi, amma da ya ga ba a taya shi da kyau ba, sai ya wuce zuwa Kano ko zai dace a saye shi a kan farashin.
“Duk da cewa na samu wadanda suka taya ni a kan Naira miliyan 10, miliyan biyar da N300,000 a Kano, amma ban sallama musu ba, saboda abin da suke son su biya bai kai abin da nake sa rai ba,” inji shi.
Matashin ya ce shi tela ne amma daga baya komai ya tabarbare mishi saboda matsalar kudade, ya rasa kwastominsa, ga shi kuma jarinsa ya karye.
A cewarsa, a halin yanzu ba shi da wani abin da zai iya dogara da shi, ballantana ya samu jarin da zai fara wata sana’a, shi ya sa ya yanke shawarar ya dora wa kansa ganye ko zai samu a saye shi a Naira miliyan 20.
A kan haka ne Aminiya ta tambaye shi abin da yake son yi da Naira miliyan 20 din da yake so a saye shi.
Sai ya kada baki ya ce, “Zan ba wa iyayena Naira miliyan 10, in ba da miliyan biyar a matsayin haraji a jihar da aka saye ni, mutumin da ya tallata ni har aka saye ni kuma zan ba shi Naira miliyan biyu, ragowar miliya uku kuma zan ba wa duk wanda ya saye ni ya ajiye a matsayin kudin kula da dawainiyata.”
A cewarsa, ya san zai rasa ’yancinsa idan aka saye shi, amma ya gwammace hakan kuma a shirye yake ya yi abin da iyayen gidansa za su sa shi.
Ya kara da cewa idan ba a samu mai sayen shi a Kano ba zai tafi wata jihar ya ci gaba da neman wanda zai saye shi.