Matashin da aka tunɓuke wa harshe ya fara iya magana
Babangida Sulaiman, matashin da wata mace ta tunɓuke wa harshe a Legas ya fara iya yin magana bayan da likitoci suka yi masa aiki har sau uku a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas. A zantawar da wakilin Aminiya ya yi da shi, Babangida na iya yin magana kaɗan-kaɗan, wacce ake iya fahimta idan an matsa […]
Babangida Sulaiman, matashin da wata mace ta tunɓuke wa harshe a Legas ya fara iya yin magana bayan da likitoci suka yi masa aiki har sau uku a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas.
A zantawar da wakilin Aminiya ya yi da shi, Babangida na iya yin magana kaɗan-kaɗan, wacce ake iya fahimta idan an matsa kusa da shi. Ya shaida mana cewa ba kowane irin abinci yake iya ci ba, domin shinkafa ce abin da ya fi ci sannan ba ya iya cin nama amma yana cin kifi idan mahaifiyarsa ta cire ƙayar jiki ta ninniƙa masa. Ya ce a kodayaushe yana fama da raɗaɗin ciwo, wanda yakan hana shi runtsawa, duk da dai a yanzu bakin nasa ba ya zubar da jini. Ya ce duk maganin da aka rubuta masa ya shanye amma hakan bai hana shi jin zafin raɗaɗin ciwon a kodayaushe ba.
“An samu akasi a aikin da aka yi mani. Maimakon gaban harshen ya miƙe a kwance sai ya tokare, ya yi ƙasa, don haka ina neman taimakon al’umma da su taimaka mani a kai ni ƙasar waje don a sake yin mani aikin harshen,” inji shi.
Mahaifiyar Babangida ta shaida wa Aminiya cewa likitocin sun yanki sassan ragowar harshen ne, inda suka yi masa dashensa a gaba, daidai inda ya tunɓuƙe. Ta ce an samu akasi a lokacin aikin domin ya yi doro daga sama, sannan gaban ya toƙare da ƙasa. Don haka ta yi kira ga ƙungiyoyin al’umma da shuwagabannin jama’a su taimaka su ɗau nauyinsa a kai sa ƙasar waje don a yi masa aiki. Ta ce sau uku ana yi masa aiki a baya, duk kuɗin da suke da shi ya ƙare. “Muna neman taimakon al’umma musanmman shuwagabaninmu na Arewa da su kawo mana ɗauki, a ceci rayuwar wannan yaro. A shekara mai zuwa muke sa ran ya fara karatun jami’a amma wannan raɗaɗin zafin da kuma rashin yin magana yadda ya kamata ba za su bari ya ci gaba da karatu ba. Don haka muna neman taimako,” inji ta.
Babangida ya buɗe wa wakilinmu bakinsa domin ganin yadda aka yi masa aikin dashen harshen. Sai dai da ya buɗe bakin nasa ba a iya ganin harshen sai ɗan alamarsa daga can cikin bakin amma duk da haka yana iya yin magana a fahimta cikin ɗan ƙaramin sauti.