Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi

Jiragensa na sama, ko da yake kanana ne, suna da bangarori masu motsi da ke yin aiki kamar na gaske.

Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi

Malam Yunusa Alfazazi, dan kimanin shekara 35 kuma mazaunin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna, ya kafa tarihi a duniyar fasaha da kirkire-kirkire, inda yake kera jiragen sama da bindigogi da sauran na’urori daga robobi da filastik.

Allah Ya albarkaci Nijeriya da mutane masu fasaha da baiwar ƙera kayayyaki ba tare da samun horo na musamman ba.

Misali, Malam Yahaya Makera da ya kafa tashar rediyo mai aiki a Kaduna da kayan aikin da ba su taka kara sun karya ba.

Haka nan, Mansur Nuhu Bamalli ya samu nasarori a fannin injiniyanci duk da ƙarancin kayan aiki da suke fama da shi da kuma rashin goyon baya na musamman.

Malam Yunusa Alfazazi na daga cikin irin wadannan matasan masu hazaka, wadanda za su iya taka muhimmiyar rawa wajen ci-gaban fasaha da kirkire-kirkire a Nijeriya idan suka samu goyon baya da tallafin da ya dace.

Duk da irin basirarsa, Yunusa Alfazazi ba injiniya ba ne kuma bai taɓa halartar wata makarantar koyon fasaha ba.

Kai! Bai ma taɓa halartar wata makarantar zamani ba. Da kansa ya koyar da kansa, ya kuma ci gaba da inganta fasahar tasa a tsawon shekaru ta hanyar gwaje-gwaje da bincike.

Duk da wannan basirar tasa, matsayin yana sana’ar tura baro ne da yin dako wajen samun na rufin asiri, duk da kasancewarsa bai taba aure ba.

Gwamna da Babban Hafsan Tsaro sun yaba masa

Ayyukan Yunusa ba na wasa ba ne, domin yana kera samfurori masu cike da tsari da fasaha, wadanda suka ja hankalin manyan mutane, ciki har da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai.

A wata ziyara da El-Rufai ya kai garin Kafanchan, ya yi mamakin fasahar Yunusa.

“Gwamna El-Rufai ya tambaye ni ko ni ne na kera jirgin saman da ya gani. Na amsa masa da eh, sai ya ba ni katin tuntubarsa domin mu yi magana kuma na ba shi kyautar helikwaftar.

“ Amma gaskiya ban kira shi ba. Wannan abin ya faru ne lokacin yana gwamna,” in ji Yunusa.

Haka nan, Janar Christopher Gwabin Musa ya yaba da fasahar matashin, tare da sayen daya daga cikin bindigogin roba da ya kera.

“Ya yaba min, ya ba ni kyauta, kuma ya karbi bindigar,” in ji Yunusa, wanda ya ce “ban samu horo na musamman a kan aikin ba.”

Ya dai dogara ne da kokarinsa da baiwarsa kawai tare da lura da yanayin abuguwan.

Ya ce, “Na fara ne da kera kananan motocin roba da bindigogi. Daga baya kuma sai na fara kera jiragen sama.”

Hazakarsa tasa ta kunsshi sarrafa abubuwa daga kayayyakin da aka yi watsi da su zuwa abubuwa masu ban mamaki ne.

Yana amfani da robar danko da filastik don kera samfurorin jiragen sama da bindigogi kala-kala da suka yi kama da na gaskiya.

Abin da ya fi burge mutane game da shi shi ne yadda ba ya amfani da na’urorin aiki na zamani.

Da kayan aiki na yau da kullum da kuma kwarewarsa yake kera kayayyaki masu tsari kamar na gaske.

Jiragensa na sama, ko da yake kanana ne, suna da bangarori masu motsi da ke yin aiki kamar na gaske.

Bindigoginsa kuwa da ya kera daga robobi da filastik, suna daukar hankali, kai ka ce bindigogi ne na gaskiya.

Zan iya fiye da wadannan —Alfzazi

Sai dai duk da kwarewarsa, Yunusa bai samu wata dama da za ta amfane shi ba har zuwa yanzu.

Wannan shi ne irin yanayin da wasu matasan Nijeriya ke fuskanta ta shi na rashin jagoranci ko tallafi daga gwamnati ko kungiyoyi masu zaman kansu, lamarin da ya haifar wa da tafiyar Yunusa cikas da kalubale.

Babban burinsa shi ne gwamnati ta dauke shi aiki a wata hukuma da ke kula da kera kayayyaki irin wadannan domin ya ba da tasa gudunmawarsa ga ci-gaban kasa.

Ya ce, “Ina jin zan iya yin fiye da abin da nake yi idan aka ba ni dama. Ina so in zama wani bangare na wani gagarumin aiki domin in taimaka wajen kera kayayyakin da za su amfanar da Nijeriya.”

Rashin tallafi

Amma saboda rashin goyon baya, yana dogaro ne da dan abin da da yake samu daga mutanen da ke sha’awar ayyukansa.

Wani lokaci kuma yana tura baro ne don yin dako domin ya samu abin da zai ci.

“Ba ni da iyali, kuma ba ni da aiki. Nakan samu wasu ’yan kudi ne daga mutanen da ke sha’awar aikina.

“Wasu lokutan kuma sai na yi dako ta hanyar tura baro nake samun abin dogaro a rayuwata. Wannan ne yake ci gaba da karfafa min gwiwa.”

‘Jami’in tsaro ya sa ni a tsaka-maiwuya’

Duk da girmamawar da yake samu, yana kuma fuskantar gargadi daga jami’an tsaro.

Ya ce, “Wani jami’in tsaro ya taba gargadina cewa in kula da kyau kada in rika yada sirrin fasahata ga mutanen da ba su dace ba.

Ya ce in kiyaye sosai kada in sayar da fasahata ga kowa.”

Matashin ya ce, wannan gargadin ya kara jefa shi cikin damuwa da rashin tabbas game da inda zai dosa yanzu da irin wannan fasahar kuma da suwa zai yi hulda har ta kai shi ga samun hadin gwiwa da mutanen da za su iya taimaka masa.

Duk da cewa yana fahimtar tasirin sirri da tsaro da ke tattare da aikinsa, amma yana gudun kada ganin baiwarsa ta tafi a banza.

 “Idan da zan samu damar yin aiki tare da hukumomin gwamnati ko masana’antu masu zaman kansu, zan iya amfani da baiwata ta hanyoyin da za su amfanar da kasa,” in ji shi.

Yadda za a ci moriyar basirar

Nijeriya tana fama da matsalar yawan kaurar masu basira zuwa kasashen waje, ko kuma rashin amfani da baiwar da ake da ita saboda rashin damarmaki.

Lamarin Yunusa misali ne na irin mutane masu hazaka da ke fuskantar kalubale a kasar da ke neman ci-gaban fasaha.

A yayin da ake kokarin kera kayayyakin soja da na tsaro a Nijeriya, ana bukatar matasan irin Yunusa su samu goyon baya, a maimakon barinsu da ake yi su kasance ba su ga tsuntsu ba su ga tarko.

Ya kamata gwamnati da kungiyoyi su fara karkatar da hankalinsu ga irin wadannan mutanen masu basira.

Idan aka ba shi horo da jagoranci, Yunusa zai iya zama kwararre a bangaren fasaha da kirkire-kirkire.

Idan aka ba shi tallafin ilimi, zai iya zurfafa bincike da kirkirar sabbin abubuwa. Idan kuma kamfanoni masu zaman kansu suka tallafa masa, zai samu damar fadada ayyukansa.

Yadda za abunkasa basirarsa

“Baya ga tallafin kudi, abin da Malam Yunusa ke bukata shi ne haduwa da kwararru a fannin injiniyanci da za su jagorance shi kan hanyoyin da suka dace.

Ta hakan, zai iya fahimtar fasaha yadda ya kamata kuma ya kera kayayyakin da za a iya fitarwa kasuwanni.

“In har aka kula da shi yadda ya kamata, na iya zama wani babbar dama ga Nijeriya a bangaren kere-kere.

“Zai iya zama jagora a fasahar kera jiragen sama da kayayyakin tsaro,” a cewar Malam Auwal Ibrahim Shehu, Daraktan kungiyar Haske Peace Debelopment Initiatibe, wata kungiya mai zaman kanta da ke Kaduna.

Malam Yunusa ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwa a kan baiwarsa, duk da matsalolin da yake fuskanta.

Yunusa ya ce, “Na san ina da wata baiwa mai amfani. Abin da kawai nake bukata shi ne dama domin in nuna duniya abin da zan iya yi.”

Ko labarinsa zai zama nasara a gare shi da kasar gaba daya, ko kuma baiwarsa zata watse, hakan ya dogara ne da yadda Nijeriya za ta dauki mataki a kan lamarinsa.