Matashin da ke zolayar Hausawa da Boko Haram ya shiga hannu a Kalaba

Wani matashi mai suna Joe Ekparawa da ya zolayi Hausawan Kalaba a unguwar Layin Bagobiri, cewa shi dan Boko Haram ne ya shiga hannu.Asirinsa ya tonu ne a ranar Litinin da ta gabata, bayan da ya zo Layin Bagobiri, ya kawo cajin batirin wayarsa ta hannu. Wasu da lamarin ya faru gabansu sun shaida wa […]

Matashin da ke zolayar Hausawa da Boko Haram ya shiga hannu a Kalaba
Matashin da ke zolayar Hausawa da Boko Haram ya shiga hannu a Kalaba

Wani matashi mai suna Joe Ekparawa da ya zolayi Hausawan Kalaba a unguwar Layin Bagobiri, cewa shi dan Boko Haram ne ya shiga hannu.
Asirinsa ya tonu ne a ranar Litinin da ta gabata, bayan da ya zo Layin Bagobiri, ya kawo cajin batirin wayarsa ta hannu. Wasu da lamarin ya faru gabansu sun shaida wa Aminiya cewa mutumin ya kawo batirin wayarsa ta hannu, da aka tambaye shi sunan da za a rubuta jikin batirin domin ya zama shaida, idan ya zo karba a ba shi, sai ya ce a rubuta Boko Haram a jikin batirin wayar tasa. Shi kuma mai cajin batiri ya ce wannan ba suna ba ne, ya dai fadi sunan da za a sanya. Mutumin ya tsaya kai da fata cewa sai dai a rubuta haka. Takaddama ta kaure tsakaninsu, lamarin da ya jawo hankalin wasu mutane da ke kusa da wurin.
Bayan hatsaniya ta kaure, Ekparawa ya nace shi sunansa ke nan kuma da shi ake kiransa a unguwarsu. Shi ne matasan unguwa suka mika shi ga Sarkin Hausawa, Alhaji Salisu Abba Lawal, domin mataki na ladabtarwa.
Majiyar ta ci gaba da cewa, nan take kuma aka kira hukuma, inda jami’an tsaro suka garzayo suka tafi da shi. Daga bisani wakilinmu ya tuntubi sarkin Hausawan domin jin gaskiyar batun, inda shi kuma ya ce: “E, hakika wani yaro dan asalin Kurosriba ya zo ya kawo cajin batirin wayarsa ta hannu, an tambaye shi sunansa da za a rubuta jikin batirin da zai zama shaida, idan ya dawo ya karba; sai ya ce a rubuta Boko Haram. Shi kuma mai cajin batirin wayar ya ce ba zai rubuta haka ba. Ni kuma ban yi kasa a gwiwa ba, nan take na sanar wa jami’an tsaro na farin kaya, suka zo suka tafi da shi.”
Ya zuwa rubuta wannan labara, matashin da ya zolayi Hausawan na can hannun jami’an tsaro suna bincikensa.