Matashin da ya dade yana neman aiki ya rasu kwana daya da samun aikin
Wani matashi dan Najeriya mai suna bictor Nwobike da ya dade yana neman aiki bayan ya kammala karatunsa ya rasu ana gobe zai fara aiki. Yadda lamarin ya faru dai kamar yadda wani makusancin bictor ya sanar shi ne, bictor ya dade yana neman aiki tun bayan da ya kammala karatunsa, ya tura takardar neman […]
Wani matashi dan Najeriya mai suna bictor Nwobike da ya dade yana neman aiki bayan ya kammala karatunsa ya rasu ana gobe zai fara aiki.
Yadda lamarin ya faru dai kamar yadda wani makusancin bictor ya sanar shi ne, bictor ya dade yana neman aiki tun bayan da ya kammala karatunsa, ya tura takardar neman aiki da yawa, amma shiru, sai kwatsam ya samu aiki, sannan aka umarce shi da ya zo ranar Litinin domin ya fara aiki, amma cikin ikon Allah sai ya rasu ranar Lahadi bayan gajeruwar jinya.