Matashin da ya je Masallacin Kudus a kafa daga Faransa

Masallacin Kudus shi ne na uku wajen falala a addinin Musulunci

Matashin da ya je Masallacin Kudus a kafa daga Faransa

Wani matashi da ya taka a kafa daga kasar Faransa ya isa Masallacin bayan wata 10.

Neil Dauxois dan shekara 26 ya yi tafiyar kilomita 3,900 inda ya ratsa ta kasashe 10 kafin ya isa Masallacin Kudus, inda ya samu gagarumar tarba daga Falasɗinawa.

Masallacin Kudus shi ne na uku wajen falala a addinin Musulunci, kuma an kwadaitar da ziyartarsa.

Yadda ake fitar da Zakkar Kono

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutun Sallah Karama

Isarsa Birnin Kudus ke da wuya, al’ummar Musulmai Falasdinawa suka yi ta maraba da shi suna gayyatar sa zuwa gidajensu, inda suka shirya masa liyafa.

Ya ce, “Da farko mahaifiyata ta damu, amma bayan da ta ga hotunana a kafofin sada zumunta, sai ta bayyana alfaharinta da ni.”

Kasashen da ya wuce bayan ya fara tafiyar daga Faransa sun hada da Italy, Slovenia, Croatia, Bosnia-Herzegovina, Montenegro, Albania, Greece, Türkiye, Cyprus da Jordan kafin ya isa birnin Kusus.

“Falasinawa da yawa sun yi ta gayyata ta zuwa gidajen; Na yi mamakin hakan, kuma na yi farin ciki sosai,” in ji shi, bayan isarsa Birnin Kudus.

Neil wanda dan asalin kasar Aljeriya ne, ya ce, burinsa na gaba shi ne karasawa zuwa kasar Saudiyya a cikin wata biyu domin yin aikin Hajji.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara